Zanga Zanga: Sanusi II Ya Koka Kan Lalata Wurin da Kakansa Ya Yi Aiki

Zanga Zanga: Sanusi II Ya Koka Kan Lalata Wurin da Kakansa Ya Yi Aiki

  • Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya ziyarci wuraren da aka yi ɓarna yayin zanga-zangar da aka yi kwanan nana jihar
  • Mai martaba Sarkin ya koka kan irin ɓarnar da aka yi tare da bayyana cewa akwai sakacin jami'an tsaro da suka bari hakan ya faru
  • Sanusi II ya ce daga cikin wuraren da aka lalata akwai inda kakansa ya yi aiki inda ya bayyana hakan a matsayin abin baƙin ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, mai martaba Muhammadu Sanusi II, ya koka kan ɓarna da satar dukiyoyin da aka yi yayin zanga-zangar da aka yi a jihar.

Sanusi II ya yi magana ne dai lokacin da ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da aka lalata yayin zanga-zangar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fadi abin da ya dace 'yan Najeriya su yi maimakon zanga zanga

Sanusi II ya koka kan barna a Kano
Sanusi II ya koka kan barnar da aka yi yayin zanga-zanga a Kano Hoto: @MasarautarKano
Asali: Twitter

Sanusi II ya ziyarci wuraren da aka lalata

Jaridar Daily Trust ta ce daga cikin wuraren da Sanusi II ya ziyarta akwai babban kantin Barakat, maɗaba'ar Kano, da cibiyar fasahar zamani ta NCC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zargi jami’an tsaro da yin sakaci wajen barin ɓarnar ta auku duk da sanarwar da suka samu kan hakan.

An lalata wurin da kakan Sanusi II ya yi aiki

Sanusi II ya ce kakansa ya yi aiki da maɗaba'ar Kano inda ya ƙara da cewa abin baƙin ciki ne wuri kamar wannan jikokinsu sun lalata shi, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

"Kamar yadda muka saba faɗa cewa duk wanda ke da hannu a cikin wannan maƙiyin Kano ne, kuma maƙiyi ne ga al’ummarta."
"Kakana ya yi aiki a nan (maɗaba'ar Kano). Abin baƙin ciki ne yadda jikokinsu suka lalata irin wannan wuri."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Sanusi II ya fadi masu laifi kan barnar da aka yi a Kano, ya yi addu'a

- Mai martaba Muhammadu Sanusi II

Gwamna Abba ya taya Sanusi II murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya cika shekara 63 a duniya, yayin da ya yi watanni biyu da komawa karagar sarki.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shiga sahun 'yan uwa, abokan arziki da kuma masoya wajen taya Sanusi II murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng