Ana Ƙoƙarin Shawo kan Ndume, Dan Majalisa ya Kara Tsige Gaskiya ga Tinubu

Ana Ƙoƙarin Shawo kan Ndume, Dan Majalisa ya Kara Tsige Gaskiya ga Tinubu

  • Dan majalisar wakilai daga jihar Anambara, Uchenna Harris Okonkwo ya tura sako na musamman ga shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Uchenna Harris Okonkwo ya yi magana ne kan halin kunci da yan Najeriya ke ciki wanda ya haifar da zanga zangar tsadar rayuwa
  • Haka zalika dan majalisar tarayyar ya yi kira na musamman ga jami'an tsaro kan yadda suke mu'amala da talakawan Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Idemili ta Kudu da Arewa ya tura sako ga Bola Ahmed Tinubu kan tsadar rayuwa.

Dan majalisar ya fadi abin da ya kamata shugaban kasa ya yi a kan halin da al'umma ke ciki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: A karshe, Ganduje ya yi magana, ya tura sako ga 'yan Najeriya

Majalisar wakilai
Dan majalisa ya tura sako ga Tinubu kan tsadar rayuwa. Hoto: Abbas Tajudden
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Uchenna Harris Okonkwo ya buƙaci jami'an tsaro su inganta aikinsu a lokutan tashin hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan majalisa: 'Ana wahala a Najeriya'

Dan majalisar wakilai daga jihar Anambara, Uchenna Harris Okonkwo ya tabbatar da cewa talakawa na shan wahalar rayuwa a Najeriya.

Hon. Uchenna Harris Okonkwo ya fadi haka ne a ranar Laraba yayin da yake fadawa shugaba Bola Tinubu matakin da ya kamata ya ɗauka.

Sakon dan majalisar Anambra ga Bola Tinubu

Saboda wahalar rayuwa da ake a Najeriya, Uchenna Harris Okonkwo ya bukaci Bola Tinubu ya yi ayyukan da za su kawo sauki ga talaka.

Leadership ta wallafa cewa Uchenna ya bukaci Bola Tinubu ya rage yadda yake kashe kudi a harkar gwamnati da yin ayyuka da gaske maimakon magana kawai.

Sakon dan majalisar ga jami'an tsaro

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan Katsina a shirgegen muƙami, ya tura saƙo

Haka zalika Hon. Okonkwo ya bukaci jami'an tsaro da su rika nuna kwarewa yayin aiki musamman tsakaninsu da talakawa.

Dan majalisar ya ce ya bai kamata a samu muzgunawa ga talakawa ba wanda dama yunwa ta gama jikkatasu.

An gano albashin yan majalisar wakilai

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilan Nakeriya ta bayyana haƙiƙanin albashin da ake biyan ƴa ƴanta a duk ƙarshen wata.

Kakakin majalisar, Rotimi Akin, ya bayyana cewa ana biyan ƴan majalisar albashin N600,000 duk wata saɓanin N900,000 da ake ta yaɗawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng