Ana Zanga Zanga, Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane, An Yi Garkuwa da Wasu Rututu a Arewa

Ana Zanga Zanga, Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane, An Yi Garkuwa da Wasu Rututu a Arewa

  • Yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe mutane shida a kauyuka huɗu da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna
  • Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutane 26 a hare-hare daban-daban da suka kai kauyukan
  • Wani mutumin yankin Aminu Khalid ya yi kira ga dakarun sojoji su tashi wani daji da ƴan bindiga ke samun mafaka wajen yin ta'asa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - ‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane shida tare da yin garkuwa da wasu 26 a lokacin da suka kai hari wasu kauyuka a ƙaramar hukumar Kauru a Kaduna.

Maharan sun aikata wannan ɗanyen aiki ne a kauyuka huɗu da suka haɗa da Sabon Gidan Libere, Ungwan Ganye, Ungwan Nabara, da Kadi duk a yankin Kauru.

Kara karanta wannan

Matasa sun fusata da kisan ɗan uwansu, sun bankawa fadar basarake wuta a Arewa

Malam Uba Sani.
Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun yi garkuwa da wasu sama da 20 a Kaduna Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun shiga kauyukan ne a hare-hare daban-daban, inda suka kashe mutane shida tare da sace mutum 26, Vanguard ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kaduna: Yadda ƴan bindiga suka shiga kauyuka

Aminu Khalid wanda ya tsallake rijiya da baya, ya ce ‘yan ta’addan sun farmaki Sabon Gida Libere a ranar Litinin, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu 23. 

Mutumin ya kuma bayyana cewa maharan sun kashe mutum uku a kauyen Unguwan Nabara.

"Har yanzun ƴan bindigar ba su tuntuɓi kauyukan ba amma garuruwa da dama sun zama kufai saboda yawaitar hare-haren ta'addanci. Ƴan bindiga suna da sansani kusa da garin Libere a dajin Agwala da ke saman tsauni.
"Ya kamata gwamnati da dakarun sojoji su shafe babin dajin da ƴan bindigar ke samun mafaka domin jama'a su samu kwanciyar hankali a kauyukansu," in ji Aminu.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame hedkwatar NLC bayan gano wani sirri kan zanga zanga

Ƴan bindiga sun tarwatsa mutane

Aminu Khalid ya ce galibin mazauna yankin sun gudu sun bar gidajensu saboda ƴan bindiga sun hana su zuwa gonakin su.

Har kawo yanzu rundunar ƴan sanda ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan wannan hari ba, rahoton Leadership.

DSS ta kai samame hedikwatar NLC

A wani rahoton na daban jami'an tsaro sun kai samame hedkwatar kungiyar kwadago ta kasa NLC a daren ranar Laraba kan zanga-zangar da ake yi a ƙasar nan.

Masu gadin wurin sun bayyana cewa jami'an sun rufe fuskokinsu a lokacin da suka shiga wurin kuma kai tsaye suka nufi ofishin shugaban NLC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262