Gaskiya Ta Bayyyana Kan Hakikanin Albashin da Ake Biyan 'Yan Majalisa
- Majalisar wakilan Nakeriya ta bayyana haƙiƙanin albashin da ake biyan ƴa ƴanta a duk ƙarshen wata
- Kakakin majalisar, Rotimi Akin, ya bayyana cewa ana biyan ƴan majalisar albashin N600,000 duk wata saɓanin N900,000 da ake ta yaɗawa
- Ya bayyana cewa ƴan majalisar suna nan a kan bakansu na rage kaso 50% na albashinsu domin rage wahalhalun da ake fama da su a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta fito ta bayyana haƙiƙanin albashin da ake biyan ƴan majalisar duk wata.
Kakakin majalisar wakilai, Rotimi Akin, ya bayyana cewa albashin ƴan majalisar duk wata N600,000 ne saɓanin N900,000 da ake ta yaɗawa.
Nawa ne albashin ƴan majalisa?
Akin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin majalisar ya jaddada ƙudirin ƴan majalisar na rage kaso 50% cikin 100% na albashinsu domin rage wahalhalun da ake fama da su a ƙasar nan, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
"Majalisar wakilai ta samu rahotannin da wasu kafafen watsa labarai ke yaɗawa kan bambanci a albashin ƴan majalisa, wanda ya yi iƙirarin cewa mun karɓi kaso 100% na albashinmu a watan Yuli."
"Rahoton ya yi iƙirarin cewa albashin da ake ba ƴan majalisa duk wata ya kai N936,979."
"Muna son mu bayyana cewa haƙiƙanin albashin da ake ba ƴan majalisa duk wata shi ne N600,000, bayan an cire kuɗin gida wanda ake biya a farkon wa'adin fara mulki."
- Rotimi Akin
Ya ƙara da cewa har yanzu majalisar tana nan kan ƙudirin da ta amince da shi a ranar, 18 ga watan Yuli wanda ya yi umarnin rage albashin ƴan majalisun da kaso 50% har na tsawon wata shida.
Tinubu ya roƙi ƴan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara kai zuciya nesa da gwamnatinsa.
Shugaban ƙasan ya ba da tabbacin cewa ƙasar nan tana samun tagamoshi inda ta fara samun ci gaba maimakon koma bayan da ta samu a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng