"Ku Amshi Tayin Gwamnati," Sarki Ya Lallashi Masu Zanga Zanga

"Ku Amshi Tayin Gwamnati," Sarki Ya Lallashi Masu Zanga Zanga

  • Zanga-zangar nuna adawa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta shiga rana ta bakwai daga cikin kwanaki 10 da za a yi ana fita tituna
  • Shugaban kasa, Bola Tinubu da mukarrabansa sun yi ta rokon matasan su yi hakuri a hau teburin tattaunawa domin share masu hawaye
  • A bangarensa, basaraken masarautar Idjerhe a Delta, Obukowho Monday Whiskey ya sake rokon matasan su amsa kiran gwamnati na tattaunawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Delta - Sarkin Idjerhe a jihar Delta, Obukowho Monday Whiskey ya goyi bayan shugaban kasa na neman tattaunawa da masu zanga-zanga.

Sarkin ya roki matasa su dakata da fitowa nuna fushinsu bisa gazawar gwamnati na inganta masu rayuwa.

Kara karanta wannan

Kano: Mabarata sun shafe kwanaki da yunwa, sun nemi a janye zanga zanga

Bola Tinubu
Basarake ya shawarci matasa su tattauna da shugaban kasa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

TABLE OF CONTENTS

Jaridar Vanguard ta tattaro sarkin ya shaidawa matasan kasar nan cewa kokensu ya isa inda ake bukata, yanzu tattaunawa ce mataki na gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yabawa wasu daga cikin matasan da su ka fito zanga-zanga cikin lumana, duk da an samu wuraren da bata-garin su ka bata lamari.

"Na yi takaicin kashe masu zanga-zanga," Sarki

Sarkin Idjerhe, Obukowho Monday Whiskey ya bayyana takaicin yadda aka zubar da jinin wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar nan, Niger Delta Today ta wallafa.

Mai martaba Idjerhe ya kara da nuna bacin rai ganin yadda wasu miyagu su ka rika lalata kadarorin jama'a da sace wasu daga cikin kayan jama'ar da ba su ji ba,ba su gani ba.

Ya ce kashe-kashe da sata da ake yi a wasu sassan kasar, ba shi ne zai magance matsalolin yunwa da fatara da ake fuskanta ba.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun harzuka, za a gudanar da makokin wadanda aka kashe

Zanga-zanga: Za a yi makokin kwanaki

A wani labarin kun ji cewa jagororin zanga-zangar adawa da manufofin Bola Tinubu za su yi makokin wasu daga cikinsu da jami'an tsaro su ka kashe.

Za a fara makokin daga ranar Laraba zuwa Juma'a domin kara jaddada rashin jin dadin matakin da gwamnati ta dauka a kan masu adawa da barinsu cikin yunwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.