Gwamnan Zamfara Ya yi Maganar Zargin Kashe ₦19.3bn kan Kayan Dafa Abinci

Gwamnan Zamfara Ya yi Maganar Zargin Kashe ₦19.3bn kan Kayan Dafa Abinci

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta yi bayani kan zarginta da aka yi da ware kudi Naira biliyan 19.3 domin kayan dafa abinci a jihar
  • Kwamishinan kasafin kudi da tsare tsare na jihar, Malam Abdulmalik Gajam ya bayyana abin da aka ware kudin dominsu
  • Malam Abdulmalik Gajam ya kuma bayyana matakin da gwamnatin jihar ta ke dauka dangane da kudin da Zamfara ke samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta yi karin haske kan zarginta da aka yi da ware makudan kudi har N19.3bn domin samar da kayayyakin girki.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa ba maganar gaskiya cikin zargin da aka yi mata kwata kwata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya ware miliyoyi domin samar da ofisoshi ga masu ba shi shawara

Jihar zamfara
Gwamnatin Zamfara ta yi bayani kan zargin ware ₦19.3bn. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa kwamishinan kasafin kudi na jihar, Malam Abdulmalik Gajam ne ya yi bayanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ware N19.3b a sayen kayan abinci?

Daily Post ta wallafa cewa kwamishinan tsare tsare da kasafin kudi na Zamfara, Abdulmalik Gajam ya ƙaryata cewa jihar ta ware kudi N19.3b ga kayan abinci a shekar 2024.

Malam Abdulmalik Gajam ya ce an ware kudin ne ga harkokin ilimi amma wanda suka wallafa labarin ba su fahimta ba.

Zamfara: 'Suna da mummunar manufa'

Kwamishinan kudin jihar, Malam Abdulmalik Gajam ya ce abin takaici ne matuka yadda wasu kafafen yada labarai suka wallafa labarin.

Malam Abdulmalik Gajam ya kara da cewa labarin karyar an yaɗa shi ne domin kawo ruɗani a cikin al'umma.

Nawa aka ware ga kayan abinci?

Gajam ya bayyana cewa an ware kudi Naira miliyan 40 ga dafa abinci a dukkan makarantun gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Bayan zanga zanga, Abba ya dauko muhimman ayyuka 7 domin farfaɗo da Kano

Ya kuma bayyana cewa gwamna Dauda Lawal ya zo Zamfara ne domin kawo gyara da toshe hanyoyin wadaƙa da kudin gwamnati.

Zamfara: PDP ta yabi Dauda Lawal

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da aka yi zanga-zanga a Najeriya, jam'iyyar PDP a jihar Zamfara ta yabawa Gwamna Dauda Lawal kan shugabancinsa.

Jam'iyyar PDP ta ce salon mulkin Lawal Dare mai kyau shi ne musabbabin rashin gudanar da zanga-zanga da aka yi a sauran jihohi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng