Allah ya baka lafiya – Zahra Buhari ga dan uwanta

Allah ya baka lafiya – Zahra Buhari ga dan uwanta

Yar Shugaban kasa kuma matar dan biloniya Ahmad Indimi wato Zahr Buhari ta yi karin haske akan labarin hatsarin dan uwanta Yusuf Buhari.

A safiyar ranar Alhamis 28 ga wata Disamba, Zahra ta wallafa a shafin ta na Intagram cewa tana mika sakon godiya ga dinbim yan Najeriya da suka taimaka da addu'o'i.

Zahra ta tabbatar ma jama'a cewa dan uwanta yana murmurewa kuma yana samun kulawa.

Allah ya baka lafiya – Zahra Buhari ga dan uwanta
Allah ya baka lafiya – Zahra Buhari ga dan uwanta

A baya Legit.ng ta rahoto cewa rashin lafiyar Yusuf Buhari, wanda ɗa ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanya mahaifiyarsa, Aisha Buhari cikin damuwa da har an kwantar da ita a asibitin Cedacrest dake birnin tarayya domin ta samu hutu wajen guje mata fadawa cikin wani hali.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sa'idu Dakingari da wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC

Rahotannin sun bayyana cewa, wannan asibitin shine inda Yusuf ke kwance ana jinyarsa bayan hatsarin babur da yayi tsautsayi a daren ranar Talatar da ta gabata, inda kusoshin gwamnati zababbu da wanɗanda aka naɗa ke ta shige da fice wajen duba shi.

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, ministoci, gwamnoni, shugaban EFCC da kuma shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki, sun kai ziyara asibitin a ranar Alhamis din da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng