Obasanjo Ya Fito Ya Fadi Gaskiya, Ya Bayyana Babban Kuskuren da Najeriya Ta Yi

Obasanjo Ya Fito Ya Fadi Gaskiya, Ya Bayyana Babban Kuskuren da Najeriya Ta Yi

  • Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya nuna cewa Najeriya ta yi babban kuskure kan ci gaba da dogaron da take yi kan ɗanyen man fetur
  • Ya bayyana cewa hakan babban kuskure ne inda ya bayar da shawarar cewa ya kamata ƙasar nan ta waiwayi harkar noma
  • Obasanjo ya koka kan yadda matasa masu ɗumbin yawa a ƙasar nan ke zaman kashe wando inda ya bayyana hakan a matsayin babbar matsala

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayyana damuwarsa kan yadda ƙasar nan ke ci gaba da dogaro kan ɗanyen man fetur, yana mai cewa hakan kuskure ne babba.

Obasanjo ya ce komai zai iya faruwa a ƙasar nan saboda zaman kashe wandon da matasa ke yi sakamakon rashin aikin yi.

Kara karanta wannan

Ba a gama da Dangote ba, Obasanjo ya tono batun cin hanci a matatun Najeriya

Obasanjo ya fadi kuskuren Najeriya
Obasanjo ya koka kan yadda Najeriya ke ci gaba da dogaro kan danyen man fetur Hoto: Phill Magakoe
Asali: Getty Images

Jaridar Nigerian Tribune ta ce Olusegun Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yu da manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olusegun Obasanjo ya faɗi kuskuren Najeriya

Ya bayyana cewa dogaron da Najeriya ke yi kan man fetur babban kuskure ne, rahoton tashar Arise tv ya tabbatar da labarin.

"Tattalin arziƙin Najeriya ba domin dogaron da yake yi kawai kan ɗanyen man fetur ba da ya bunƙasa sosai."
"Na yi amanna cewa mun yi babban kuskure ta hanyar dogaro da man fetur kaɗai. Muna da abu mai muhimmanci watau iskar gas, amma muna ɓarnatar da shi a iska."
"Matasanmu ba su yin komai. Ba su yin komai ne saboda ba su da sana'ar yi. Ba a ba su tallafi ba kuma ba a ba su aiki ba."
"Muna cikin babbar matsala. Addu'a ta ita ce Allah ya sanya mu yi abin da ya dace kafin lokaci ya ƙure."

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fadi masu adawa da matatar man Dangote, 'yan Najeriya sun yi martani

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya buƙaci a koma harkar noma

Obasanjo ya bayyana cewa ya kamata a ce Najeriya ta mayar da hankali sosai a kan noma maimakon ɗanyen man fetur.

"Mun yi watsi da noma wanda zai iya zama babban abin zuba hannun jarinmu."

- Olusegun Obasanjo

Karanta wasu labaran kan Obasanjo

Obasanjo ya yi magana kan matatun Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda cin hanci ya dabaibaye harkar mai a Najeriya.

Cif Olusegun Obasanjo ya fadi haka ne yayin da yake magana a kan yadda matatun man fetur suka gaza gyaruwa a Najeriya tsawon shekaru.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng