Sunayen Jihohi da Bayanan 'Yan Siyasan Arewa da Ake Tuhuma kan Daga Tutocin Rasha
- Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro sun fara bincikar wasu 'yan siyasa hudu daga Arewa kan zanga-zangar yunwa da ake gudanarwa
- An ce ana tuhumar 'yan siyasar ne bisa zarginsu da hannu a daga tutocin kasar Rasha da masu zanga-zanga ke yi a wasu jihohin Arewa
- Rahoto ya nuna cewa 'yan siyasar dai sun fito ne daga jihohin Katsina, Kaduna da Kano, kuma sun taka rawa mai girma a zaben 2023
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jami'an tsaron Najeriya suna kan tuhumar akalla 'yan siyasa hudu daga shiyyar Arewa kan zargin daukar nauyin daga tutar kasar Rasha da masu zanga-zanga ke yi.
An ruwaito cewa jiga-jigan 'yan siyasar sun fito ne daga jihohin Katsina, Kaduna da kuma Kano.
Tutar Rasha: Ana bincikar 'yan siyasar Arewa
Majiyoyi da dama sun shaidawa jaridar The Punch cewa ana zargin 'yan siyasar da hannu a ingiza masu zanga-zanga su daga tutar kasar wajen a Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda ba a bata hurumin yin magana kan lamarin ba ta ce:
"An gano manyan masu daukar nauyin daga tutar har mutum hudu. Sun kasance manyan 'yan siyasa ne daga Katsina, Kano da Kaduna kuma jami'an tsaro na bincikarsu.
"Wadannan jiga-jigan sun taka muhimmiyar rawa a babban zaben shekarar 2023 da ya gabata."
Ana zargin 'yan siyasan da karbo kwangila
Wata majiyar, wadda ita ma ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa:
"Akwai hujjoji da suka nuna cewa 'yan siyasar da aka bincika sun karbo kwangila daga wata kasa a Yammacin Afrika da Turai domin a daga tutar Rasha kamar yadda aka gani.
"Suna so ayi hakan a Najeriya kamar yadda aka yi a wasu kasashen."
A ranar Litinin ne aka ruwaito cewa zanga-zangar yunwa ta rikide zuwa wani abu na daban yayin da aka rika ganin wasu masu zanga-zanga daga Arewa suna daga tutar Rasha.
An daga tutar rasha a Kaduna
Legit Hausa ta ruwaito cewa masu zanga-zanga a Kaduna dauke da tutocin Rasha sun hau kan manyan titunan birnin jihar suna ihun "Ba mu yi," "Tinubu ya sauka," da sauransu.
Har ila yau, a jihar Kadunan ne aka ga masu zanga-zangar na satar kadarorin gwamnati da na gama garin mutane yayin da wasu suka yi dare-dare kan motar 'yan sanda.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng