'Za Mu Dawo': APC Ta Tsure, Matasan da Suka Kona Sakatariya Sun Tura Sakon Barazana

'Za Mu Dawo': APC Ta Tsure, Matasan da Suka Kona Sakatariya Sun Tura Sakon Barazana

  • Jam'iyyar APC ta yi martanin bayan kona sakatariyarta da masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa suka yi a ranar Talata
  • APC ta zargi cewa ana so a hana ta samun cigaba ne da kuma adawa da jagorancin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke yi
  • Matasan sun tura barazana ga jam'iyyar bayan kona mata sakatariyar wanda hakan yasa ta dauki matakin sanar da yan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Jam'iyyar APC ta nuna damuwa kan barazana da waɗanda suka kona mata sakatariya suka yi a Fatakwal.

Jam'iyyar ta yi zargin cewa masu adawa da shugaban kasa Bola Tinubu ne suka kai mata harin a sakatariya.

Kara karanta wannan

Kano: An kama hatsabibin 'barawon' da ya fitini mutane da fashi zai tsere bayan sace N15m

Shugaban APC
Matasa sun aike barazana bayan kona sakatariyar APC. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban riko na jam'iyyar a Rivers, Tony Okocha ne ya yi bayanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa sun yi wa jam'iyyar APC barazana

Shugaban riko na APC a jihar Rivers, Tony Okocha ya bayyana cewa matasan da suka kona musu sakatariya sun bar musu sakon cewa za su dawo.

Tony Okocha ya ce hakan na nuni da cewa APC na cikin barazana kan yiwuwar kai mata sababbin hare hare a jihar Rivers.

A karkashin haka ne jam'iyyar APC ta bukaci yan sanda sun kara matakan tsaro a kusa da sakatariyar domin tattabatar da ba a sake kai musu hari ba.

'Ana son hana mu cigaba' inji APC

Cif Tony Okocha ya ce harin da aka kai musu a sakatariya yunkuri ne na hana su kara bunkasa a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

"Ba za mu fasa ba," Kungiyar matasa ta dage kan cigaba da zanga zanga

Shugaban ya kara da cewa suna zargin hakan kokari ne na hana tauraron shugaba Bola Tinubu haskawa a fadin jihar.

Daily Post ta wallafa cewa Cif Tony Okocha ya ce harin ba zai sa su yi kasa a gwiwa ba, ya ce za su cigaba da zama sahun gaba a siyasar jihar Rivers.

Jam'iyyar APC ta zauna da Ali Ndume

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta zauna da sanata mai wakiltar Borno ta Tsakiya, Sanata Ali Ndume, bisa kalaman da ya yi a kan shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa Ali Ndume ya ba da haƙuri kan kalaman da ya yi a baya inda ya fita fili yana sukar gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng