Zanga Zanga: Jigon APC Ya Fadi Abin da Ya Dace Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi
- Kalaman da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya yi kan zanga-zanga na ci gaba da tayar da ƙura a ƙasar nan
- Wani babban jigo s jam'iyyar APC mai mulki ya buƙaci Akpabio da ya yi murabus daga muƙaminsa sannan ya ba ƴan Najeriya haƙuri
- Jonathan Vatsa ya bayyana cewa babban kuskure ne a ce mutum irin Akpabio ne yake shugabantar majalisar dattawa a gwamnatin APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Wani jigon jam’iyyar APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya buƙaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya yi murabus.
Jonathan Vatsa ya buƙaci Akpabio ya yi murabus ne saboda kalaman da ya yi kan masu zanga-zanga a faɗin ƙasar nan.
Jigon APC ya caccaki Godswill Akpabio
Jigon na APC a cikin wata sanarwa ranar Talata, ya bayyana kalaman na Akpabio a matsayin abin kunya ga jam'iyyar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙara da cewa kalaman sun sake bayyana ɗabi'ar 'ci' da jam'iyyar PDP ta saba da ita inda daga nan Akpabio ya tsallako ya dawo APC, rahoton jaridar The Sun ya tabbatar.
Tsohon kwamishinan yaɗa labaran na jihar Neja ya buƙaci shugaban majalisar dattawan ya nemi afuwar ƴan Najeriya.
Akpabio: APC ta yi kuskure a majalisa
"Babban kuskure ne kuma rashin adalci ne ga ƙasar nan a ce an ba wani mutum kamar Akpabio muƙamin shugaban majalisar dattawa a gwamnatin APC. Wannan dalilin ya sa wannan gwamnatin ba za ta taɓa ganin daidai ba."
"APC a matsayin ta na jam'iyya ta koma hannun waɗanda ƴan Najeriya suka gaji da su bayan sun buƙaci samun sauyi a 2015. Sun cika cikinsu kuma suna so su ci gaba da cika cikinsu kamar yadda Akpabio ya gayawa ƴan Najeriya."
"Akpabio wanda ya cika cikinsa a shekara 16 na gwamnatin PDP yana so ya ci gaba da cika cikinsa a gwamnatin APC."
"Ya kamata wannan jam'iyyar ta fara dawo da ƙimarta domin samun yardar ƴan Najeriya kafin 2027. Dole hakan zai fara da yin murabus ɗin Akpabio domin mu nunawa ƴan Najeriya cewa da gaske muke yi."
- Jonathan Vatsa
Shehu Sani ya faɗi hanyar tsige Akpabio
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana hanyar da za a iya bi domin tsige Godswill Akpabio daga shugabancin majalisar dattawa.
Shehu Sani ya bayyana cewa shirin yana buƙatar haɗin kan sanatoci sannan idan aka samu matsala za a iya dakatar da wanda ya kawo batun tsigewar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng