Ogun: Hukumar Zabe Ta Sanar da Ranar Zaben Ciyamomi, an Kafawa Jam’iyyu Sharudda
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta Ogun ta shirya gudanar da zaben kananann hukumomi a jihar kamar yadda sanarwa ta nuna
- Bayanai sun ce OSIEC, ta sanya ranar 16 ga watan Nuwamban 2024 domin gudanar da zaben a ƙananan hukumomi 20 na jihar
- Hukumar ta kafa sharuddan fara yakin neman zabe da kuma gudanar da zaben fidda gwani ga jam'iyyun siyasa da za su gwabza
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ogun - Hukumar zabe mai zaman kanta a Ogun (OSIEC) ta sanya ranar 16 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.
A ranar 11 ga watan Yuli ne kotun koli ta yanke hukuncin cewa daga yanzu gwamnatin tarayya ta rika biyan kananan hukumomi kudinsu kai tsaye.
Hukumar zabe ta kafawa jam'iyyu sharadi
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa kotun ta kuma umurci jihohi da su tabbatar da cewa an zabi shugabannin kananan hukumominsu ta hanyar dimokradiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, hukuncin kotun ya umarci gwamnatin tarayya da ta daina biyan kason kananan hukumomi a jihohin da ke amfani da shugabannin riko.
A wata sanarwa da shugaban hukumar OSIEC, Babatunde Osibodu ya fitar a ranar Talata, ya ce jam’iyyun siyasa za su fara yakin neman zabe a ranar 9 ga watan Agusta.
Edo: An sanya ranar zaben ciyamomi
Osibodu ya kara da cewa za a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyun ne tsakanin ranar 26 ga watan Agusta zuwa 9 ga watan Satumba, inji rahoton The Punch.
Sanarwar ta kara da cewa:
"Za a fitar da ka'idojin gudanar da zabe ta taron masu ruwa da tsaki ranar Alhamis 8 ga Agusta, yayin da za fara yakin neman zabe na jam'iyyun a ranar 9 ga watan Agusta.
"Jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaben fidda gwani na 'yan takararsu daga ranar Litinin 26 ga watan Agusta zuwa Litinin 9 ga Satumba, 2024."
An ce zababbun shugabannin rikon kananan hukumomi masu barin gado a jihar sun kammala wa’adinsu kimanin mako guda da ya gabata.
An sanya ranar zaben ciyamomi a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta a Kano ta sanya ranar da za ta gudanar da zaben kananan hukumomi 44 na jihar.
Da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Kano, shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ya ce a za gudanar da zaben ne ranar 30 ga watan Nuwamban 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng