Jerin Jagororin Zanga Zanga da Jami'an Hukumar DSS Suka Cafke

Jerin Jagororin Zanga Zanga da Jami'an Hukumar DSS Suka Cafke

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumomin Najeriya sun cafke tare da tsare wasu daga cikin jagororin zanga-zangar da ake yi ta #EndBadGovernance.

Jagororin zanga-zangar waɗanda galibinsu matasa ne, jami’an ƴan sanda ko kuma jami’an tsaro na farin kaya (DSS) ne suka kama su saboda zanga-zangar da ake yi ta nuna adawa da halin matsin tattalin arziƙi.

Jagororin zanga-zanga da DSS suka cafke
Jami'an DSS sun cafke wasu daga cikin jagororin zanga-zanga Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jagororin zanga-zanga da aka cafke

A cikin wannan rahoton, Legit Hausa ta yi ƙarin haske kan jagororin zanga-zanga da aka kama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Bashir Abubakar

A watan Yuli ne dai hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta cafke wani matashi, Bashir Abubakar, wanda aka kama a Kano bisa goyon bayansa ga zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Matasan jiha sun janye zanga zanga, sun bayyana matakin da za su ɗauka

A lokacin da aka cafke Bashir Abubakar ana cikin shirye-shiryen fara zanga-zangar ne.

Sai dai, Omoyele Sowore a wani rubutu a shafinsa na X ya ce an saki Abubakar bayan da hukumar DSS ta ce ta umarce shi da ya kawo rigunan da ya buga yana tallata zanga-zangar da ake shirin yi ta #EndBadGovernance a faɗin ƙasar nan.

2. Kabir Shehu Yandaki da Habibu Ruma

A ranar Juma'a, 2 ga watan Agustan 2024 jamian hukumar DSS suka yi caraf da matasan da suka jagoranci zanga-zanga a jihar Katsina.

An gayyaci shugabannin zanga-zangar "Struggle for Good Governance"; Kabir Shehu Yandaki da Habibu Ruma zuwa ofishin DSS da ke Katsina, inda daga bisani aka tsare su.

3. Babatunde Oluajo

A ranar Talata, 6 ga watan Agusta, ƙungiyar CDWR, ta yi kira da a saki Babatunde Oluajo da wasu masu fafutuka da hukumar DSS ta kama a zanga-zangar ba tare da wani sharaɗi ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Jami'an DSS sun kama masu ɗaukar nauyin telolin tutar Rasha a Kano

Ƙungiyar a cikin wata sanarwa da Bosah Chinedu, kakakinta ya sanyawa hannu, ta yi kira ga shugabannin ƙungiyoyin NLC da NBA da su fito fili su yi Allah-wadai da wannan zaluncin da ake yi wa masu zanga-zangar.

Hakazalika, ƙungiyar 'Take It Back' ita ma ta yi Allah wadai bisa kamun da aka yiwa ɗan fafutukar.

4. Adaramoye Michael Lenin

A ranar Litinin, 5 ga watan Agusta ne labari ya bayyana cewa jami’an DSS sun kama Adaramoye Michael Lenin, ɗaya daga cikin jagororin zanga-zangar #EndBadGovernance.

Ko da yake hukumar ta DSS ta ce Lenin ba ya hannun ta, wani ɗan jarida kuma mai fafutuka, Abiodun Sanusi, ya dage cewa jami'an DSS ne suka ɗauke shi bayan dira a gidansa da misalin ƙarfe 2:00 na dare.

Ƴan sanda sun cafke masu zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun tarwatsa tare da cafke mutum uku cikin masu zanga-zanga suka fito ranar Litinin, 5 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta ƙara ɗaukar zafi, matasa sun tafka ɓarna a hedkwatar jam'iyyar APC

Masu zanga-zangar sun fito ne a yankin Karu na birnin Abuja domin ci gaba da nuna adawa kan halin ƙuncin da ake fama da shi a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng