An Shiga Fargaba, Masu Zanga Zanga Sun Yi Ƙawanya a Gidan Ministan Tinubu
- Rahotanni da suke fitowa daga Fatakwal na nuni da cewa masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa sun kewaye gidan Nyesom Wike
- An ruwaito cewa masu zanga zangar a jihar Rivers sun kewaye gidan ministan harkokin Abujan a Rivers suna wakoki daban-daban
- Hakan na zuwa ne bayan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da matasa ke yi a kusan dukkan jihohi ta shiga kwana na shida a yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Matasa sun cigaba da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a jihohin Najeriya daban-daban.
A yau Talata an samu rahotanni kan cewa masu zanga zangar sun kewaye gidan ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike.
Jaridar Punch ta wallafa cewa masu zanga zangar sun kewaye gidan ministan ne da ke Fatakwal a jihar Rivers.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga zanga a gidan Nyesom Wike
Masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa sun dura gidan Nyesom Wike a Fatakwal suna dauke da alluna daban daban.
Hakan na zuwa ne yayin da matasa ke cigaba da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa fadin Najeriya.
Me matasa ke cewa a gidan Wike?
Rahotanni sun nuna cewa matasan na rera tsohon taken Najeriya suna ihu a kusa da gidan ministan.
Haka zalika an ruwaito cewa suna ihu suna daga murya a wajen cewa 'Nan ne gidan Wike, nan ne gidan Wike.'
Matasa sun shiga cikin gidan Ministan?
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa yayin da matasa masu zanga zangar suka isa gidan akwai tarin jami'an tsaro.
Wanda hakan na nuni da cewa ba lallai su samu damar shiga gidan ko yin barna ba kamar yadda aka samu barna a wasu wurare.
Zanga zanga: Sheikh Gumi ya yi magana
A wani rahoton, kun ji cewa babban malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana kan dawo da tallafin man fetur.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce wannan ita ce hanya mai sauki wajen dakatar da matasa masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng