Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Kwakkwaran Mataki kan Masu Daukar Nauyin Zanga Zanga
- Gwamnatin tarayya na ci gaba da ɗaukar matakai kan zanga-zangar da matasa ke gudanarwa a faɗin ƙasar nan a halin yanzu
- Hukumar shige da fice (NIS) ta bayyana cewa ta sanya masu ɗaukar nauyin zanga-zangar cikin jerin waɗanda ake nema ruwa a jallo
- Shugabar NIS, Kemi Nandep, ta bayyana cewa da zarar sun shigo ƙasar nan za a cafke su domin miƙa su zuwa ga hukumomin da suka dace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (NIS) ta yi magana kan masu ɗaukar nauyin zanga-zangar #EndBadGovernance wacce ake yi a faɗin ƙasar nan.
Hukumar ta bayyana cewa ta sanya masu ɗaukar nauyin zanga-zangar cikin jerin mutanen da take nema ruwa a jallo.
Za a cafke masu ɗaukar nauyin zanga-zanga
Kwanturola janar ta hukumar NIS, Kemi Nandap, ta bayyana hakan a hedkwatar tsaro da ke Abuja a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kemi Nandep ta bayyana cewa masu ɗaukar nauyin zanga-zangar da ke zaune a ƙasashen waje, za a yi caraf da su da zarar sun shigo ƙasar nan, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Ta bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kammala wani muhimmin taro da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa, ya yi tare da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasa.
"Akwai masu ɗaukar nauyin zanga-zanga da ke zaune a ƙasashen waje, mun sanya su cikin waɗanda ake nema ruwa a jallo."
"Za a sanar da mu da zarar sun yi ƙoƙarin shigowa cikin ƙasar nan, sannan za a cafke su domin miƙa su zuwa hannun hukumomin da suka dace."
- Kemi Nandap
An tsaurara matakan tsaro a Najeriya
Shugabar ta hukumar shige da ficen ta bayyana cewa sakamakon zanga-zangar da ake yi, an tura ƙarin jami'ai zuwa kan iyakokin ƙasar nan da filayen jiragen sama domin tabbatar da tsaro.
A cewarta hukumar ta kuma ƙara ɗaukar matakai domin tabbatar da cewa wasu ƴan ƙasashen waje ba su shigo cikin ƙasar nan ba.
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Zanga zanga: Iyalan matashin da aka kashe a Kano sun mika bukata 1 ga gwamnati
- Zanga zanga: "Mun tsaurara matakan tsaro," Gwamnatin Kano ta sassauta dokar hana fita
- "Ba za mu fasa ba," Kungiyar matasa ta dage kan cigaba da zanga zanga
ECOWAS ta magantu kan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ECOWAS ta tsoma baki kan zanga-zanga da ake cigaba da yi a Najeriya na tsawon kwanaki shida.
Ƙungiyar ta nuna damuwa kan yadda aka yi ta samun tashe-tashen hankula da rasa rayuka da dukiyoyi sakamakon zanga-zangar da ake yi saboda nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng