Matasan Jiha Sun Janye Zanga Zanga, Sun Bayyana Matakin da Za Su Ɗauka

Matasan Jiha Sun Janye Zanga Zanga, Sun Bayyana Matakin da Za Su Ɗauka

  • Jagororin da suka shirya zanga-zanga a jihar Legas sun sanar da janyewa domin duba ci gaba da suka samu tun da aka fara zuwa yau
  • Kwamared Hassan Taiwo Soweto, ɗaya daga cikin jagororin zanga-zanga ya ce ba za su ji tsoron barazanar hukumomin tsaro ba
  • Tun farko dai kwamishinan ƴan sandan Legas ya ce duba da jawabin shugaban kasa, a yanzu haramun ne wani ya fita zanga-zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Lagos: Jagororin da suka shirya zanga-zanga sun sanar da dakatar da ita na kwana ɗaya a jihar Legas domin tantance ci gaban da suka samu tun daga ranar farko.

Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar mai taken, "EndBadGovernance" a jihar Legas, Kwamared Hassan Taiwo Soweto ya sanar da hakan.

Kara karanta wannan

Legas: 'Yan daba sun kai mamaya kusa da ofishin gwamna, an tarwatsa masu zanga zanga

Masu zanga zanga.
Ana tsammanin matasa sun janye zanga-zangar yunwa a jihar Legas Hoto: Umar Aliyu
Asali: Facebook

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, Kwamared Hassan Taiwo ya ce masu zanga zangar ba su jin tsoron baranzanar jami'an tsaro, sun janye ne kawai don ra'ayin kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun sanar da janye zanga-zanga

Hassan Taiwo ya mayar da martani ga kalaman kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Adegoke Fayoade, wanda ya ce an haramta zanga-zanga a duka sassan jihar.

A wata hira da yammacin Litinin, kwamishinan ƴan sandan ya ce an dakatar da zanga-zangar ne bayan jawabin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kwamishinan ƴan sandan Legas ya ce:

"Jagororin zanga-zangar sun yanke hukuncin janyewa domin ba shugaban ƙasa damar biyan buƙatunsu. Don haka babu sauran taruwa a filin shakatawa na Gani Fawahimi a Ojota ko wani wuri na daban."

Masu zanga-zanga sun maida martani

Da yake martani ga CP Fayoade, shugaban masu zanga-zangar ya ce matasa ba za su ji tsoro ko fargabar barazanar ƴan sanda ba.

Kara karanta wannan

Bayan Legas: Matasan wata jihar Kudu sun ji kiran Tinubu, sun dakatar da zanga zanga

Ya ce masu zanga-zangar sun yanke shawarar hutawa ranar Talata domin su samu damar kara shiryawa, Channels tv ta ruwaito.

A cewarsa, sun cimma matsayar daukar hutun ne a ranar Litinin a filin zanga-zangar, amma hakan ba yana nufin an dakatar da zanga-zangar ba ne.

"Doka ta bamu ƴancin yin zanga-zangar lumana, mun ɗauki hutun rana ɗaya ne domin mu sarara mu duba ci gaban da aka samu kuma mu ƙara shiri.
"Ba zamu ji tsoron kowace barazana ba, za mu sanar da mataki na gaba a yau Talata," in ji shi.

Gwamna zai ba matasa N1.3bn

A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Ebonyi ya nuna farin ciki bisa yadda matasa suka masa biyayya, suka ƙi shiga zanga-zangar da aka fara a Najeriya.

Gwamna Francis Nwifuru ya bayyana cewa gwamnati ta ware N1.3bn domin rabawa matasa 1,300 tallafin da za su kama sana'a su dogara da kansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262