Obasanjo Ya Fadi Masu Adawa da Matatar Man Dangote, 'Yan Najeriya Sun yi Martani

Obasanjo Ya Fadi Masu Adawa da Matatar Man Dangote, 'Yan Najeriya Sun yi Martani

  • Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa masu cin gajiyar shigo da mai za su yi kokarin cin dunduniyar matatar Dangote
  • Olusegun Obasanjo ya idan har ta samu nasara, to ya kamata matatar Dangote ta zamo abin alfahari da zama tsani ga masu zuba jari a gida da waje
  • Tsohon shugaban kasar ya caccaki 'yan Najeriya bisa yadda suka dogara da mai, inda ya ce an yi watsi da gas, noma da rashin kula da matatu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa masu samun arziki daga shigo da mai ba za su bari matatar man Dangote ta yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

Olusegun Obasanjo ya yi wannan ikirarin ne bayan da Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote ya yi zargin cewa wasu 'kusoshi' na son kawo cikas ga matatarsa.

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi magana kan matatar man Dangote
Obasanjo ya ce masu samun kudi a harkar shigo da mai ba za su kyale matatar Dangote ta yi nasara ba. Hoto: @Riccardo Savi/@Naija_PR
Asali: Twitter

Obasanjo ya magantu kan matatar Dangote

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi kan al'amuran da ke tafiya a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Sa hannun jarin Aliko a harkar matatar mai, idan ya yi nasara, zai zama abin afahari kuma dama ga ‘yan Najeriya da wadanda ba ‘yan Najeriya ba su sa hannun jari a cikin kasar.
"Idan masu siyarwa ko shigo da mai Najeriya suka ga za su iya rasa makudan kudin da suke samu daga harkallarsu to za su yi duk mai yiwuwa domin kawo cikas ga matatar."

- A cewar Olusegun Obasanjo.

Obasanjo ya caccaki Najeriya kan dogaro da mai

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Tinubu ya dauki alkawari 1 yayin da ya fallasa shirin wasu 'yan siyasa

Obasanjo ya soki yadda Najeriya ta mayar da hankali kan man fetur, inda ya bayyana cewa kasar ta tafka babban kuskure ta hanyar yin watsi da iskar gas da noma, inji rahoton Channels TV.

A cewar Obasanjo:

"Mun yi kuskure ta hanyar mayar da hankalinmu kan man fetur, mun yi watsi da iskar gas da kuma noma, wadanda ya kamata su kasance a gaba gaba wajen dawo da tattalin arziki."

Ya bayyana kokarinsa na shigar da kamfanin Shell a harkokin matatun man Najeriya, amma kamfanin ya ki amincewa, saboda cin hanci da rashawa da kuma rashin kulawa a kasar.

Dangote: An yi wa kalaman Obasanjo martani

Somtoo Obiagbaso ya yi sharhi a Facebook:

"Shin wadannan mutanen sun fi gwamnatin tarayya karfin iko ne?."

Bánkólé Ikúsìkà ya ce:

"A soke lasisin shigo da mai idan ba za su iya shiga hankalinsu ba. Shikenan!"

Ighodaro Kelley Osayemwenre ya ce:

Kara karanta wannan

Kwana 1 da zanga zanga, gwamnatin Tinubu ta bude kofa kan bukatun talakawa

"Wadannan su ne dai mutanen da suka ci dunduniyar matatun Najeriya suka hana su aiki domin cimma wata muguwar manufarsu."

Majalisar Wakilai ta wanke matatar Dangote

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta ce binciken da ta yi ya gano cewa dizal da matatar Dangote ke fitarwa ya na da inganci.

Majalisar ta ce ikirari da zargin da NMDPRA ta yi na cewa dizal din Dangote ba shi da kyau karya ne, inda ta ce ya fi wanda ake shigo da shi daga waje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.