Jerin Sanatoci da 'Yan Majalisun Tarayya 26 da Suka Rasu cikin Shekara 9 da Suka Gabata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - A cikin shekara tara da suka gabata (2015 zuwa 2024), Najeriya ta rasa ƴan majalisar dokoki ta tarayya da ke kan kujera aƙalla mutum 26.
Daga cikinsu akwai sanatoci takwas da ƴan majalisar wakilai mutum 18 waɗanda duk sun rasu ne a lokacin da jam'iyyar APC ke mulki a ƙasar nan.
Jaridar Leadership ta ce bincike ya nuna cewa ƴan majalisun waɗanda suka fito daga yankunan ƙasar nan, sun rasu ne sakamakon rashin lafiya yayin da guda ɗaya ya rasu saboda raunin harbin bindiga.
Sanatocin da suka rasu daga 2015 zuwa 2024
Sanatoci tara da ke kan kujera ne suka riga mu gidan gaskiya daga shekarar 2015 zuwa 2024. Ga jerinsu a nan ƙasa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Sanata Ahmed Zanna
Sanata Ahmed Zanna, wanda ke wakiltar Borno ta Tsakiya, ya rasu ne a shekarar 2015 yana da shekara 59, cewar rahoton jaridar Premium Times.
Kafin rasuwarsa ya yi fama da rashin lafiya wanda ya sanya ya samu ciwon sashi. Ya rasu bayan ya dawo daga Amurka inda ya je neman lafiya.
2. Sanata Isiaka Adetunji Adeleke
Sanata Isiaka Adetunji Adeleke ya yi sanata sau biyu kafin rasuwarsa. Ya wakilci Osun ta Yamma a majalisar dattawa a ƙarƙashin inuwar PDP a zaɓen 2007, an sake zaɓensa a zaɓen 2015 ƙarƙashin APC.
Sanatan ya rasu sakamakon ciwon zuciya a ranar 23 ga watan Afirilun 2017 a asibitin Biket da ke Osogbo a jihar Osun.
3. Sanata Ali Wakili
Sanata Ali Wakili wanda tsohon kwanturola na kwastam ne ya rasu lokacin da yake wakiltar Bauchi ta Yamma a majalisar dattawa a ranar, 17 ga watan Maris 2018.
4. Sanata Benjamin Uwajumogu
Sanata Benjamin Uwajumogu ya rasu ne a ranar, 18 watan Disamban 2018 sakamakon rashin lafiya. Ya wakilci Imo ta Arewa a majalisar.
5. Sanata Ignatius Datong Longjan
Sanata Ignatius Datong Longjan ya je majalisa ne a shekarar 2019. Ya wakilci Plateau ta Kudu a majalisar kafin rasuwarsa a shekarar 2020.
Ya riƙe muƙamin mataimakin gwamnan jihar Plateau daga shekarar 2011 zuwa 2015.
6. Sanata Rose Okoji Oko
Sanata Rose Okoji Oko wacce ta wakilci Cross Rivers ta Arewa ta rasu ne a ranar 23 ga watan Maris 2020.
7. Sanata Adebayo Sikiru Osinowo
Sanata Adebayo Sikiru Osinowo wanda ya wakilci Legas ta Gabas ya rasu ne a ranar, 15 ga watan Yunin 2020.
8. Sanata Patrick Ifeanyi Ubah
Sanata Patrick Ifeanyi Ubah wanda sanannen ɗan kasuwa ne ya rasu ne a birnin Landan a ranar, 27 ga watan Yulin 2024.
Ƴan majalisar wakilai da suka rasu daga 2015 zuwa 2024
9. Honarabul Olatoye Temitope Sugar
Honarabul Olatoye Temitope da ke wakiltar Lagelu/Akinyele ya rasu ne a ranar, 9 ga watan Maris 2019.
An harbe shi ne a ƙauyen Lalupon da ke ƙaramar hukumar Lagelu da ke jihar Ibadan. An garzaya da shi asibiti a Ibadan inda ya rasu a can.
10. Honarabul Ja'afaru Iliyasu
Ja'afaru Iliyasu wanda ya wakilci mazaɓar Magama/Rijau a majalisar wakilai daga jihar Neja ya rasu ne a watan Satumban 2019.
11. Hon Mohammed Adamu Fagen Gawo
Honarabul Mohammed Adamu Fagen Gawo ya rasu ne yayin da ke wakiltar mazaɓar Garki/Bubara daga jihar Jigawa.
Ya rasu ne a shekarar 2019 a Dubai bayan yaje neman lafiya.
12. Honarabul Bello Sani
Bello Sani wanda ya wakilci Mashi/Dutsi daga jihar Katsina ya rasu yana da shekara 51 a ranar, 15 ga watan Fabrairun 2017.
13. Honarabul Umar Buba Jibril
Umar Buba Jibril wanda ya wakilci Lokoja/Kogi/Koton Karfe daga jihar Kogo ya rasu yana da shekara 57 a wani asibiti a birnin tarayya Abuja.
14. Honarabul Elijah Adewale
Elijah Adewale kafin rasuwarsa shi ne ɗan majalisa mai wakiltar Ifako Ajaiye daga jihar Legas.
Ya faɗi ya rasu ne da safiyar ranar, 21 ga watan Yulin 2016 a gidansa da ke Abuja.
15. Honarabul Musa Baba-Onwama
Honarabul Musa Baba-Onwama ya wakilci Nasarawa/Toto daga jihar Nasarawa. Ya rasu yana da shekara 50 a duniya.
Sauran su ne:
16. Honarabul Abdullahi Wamakko
17. Honarabul Yuguda Hassan Kila
18. Prestige Ossy
19. Adebayo Omolafe
20. Haruna Maitala
21. Sulaiman Lere
22. Ekpenyong Bassey
23. Abdulkadir Danbuga
24. Isa Dogonyaro
25. Musiliudeen Akinremi
26. Abubakar Adams Ekene
Tinubu ya dawo da tallafin man fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa an dawo da tallafin fetur da Shugaba Bola Tinubu ya cire a shekarar 2023.
Olusegun Obasanjo ya ce Shugaba Tinubu ya dawo da biyan tallafin fetur din ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da kasar ke fuskanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng