Jagora a APC Ya Dauko Hanyar Dakile Zanga Zanga, Ya Tura Sako ga Mai Tunzura Matasa

Jagora a APC Ya Dauko Hanyar Dakile Zanga Zanga, Ya Tura Sako ga Mai Tunzura Matasa

  • Wani jagora a jam'iyyar APC ya ɓullo da hanyar ganin ya shawo kan masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya
  • Jagoran ya dauki matakin ne bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya yi kira ga matasan Najeriya amma sun ki sauraronsa
  • Matasa sun fara zanga zanga a Najeriya ne tun ranar 1 ga watan Agusta domin kawo karshen tsadar rayuwa a fadin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Wani jagoran matasan jami'yyar APC mai suna Kwamared Olamide Lawal ya fara ƙoƙarin shawo kan masu zanga zanga.

Olamide Lawal ya fara kira ga shugabannin zanga zangar domin ganin sun hakura da fita kan tituna.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Zanga zanga ta birkice, matasa sun toshe hanyoyi

Shugaba Tinubu
APC ta fara lallaba masu zanga zanga. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta wallafa cewa Kwamared Olamide Lawal ya bayyana haɗuran da za a samu idan aka cigaba da yin zanga zangar a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagoran APC ya yi kira ga Sowore

Kwamared Olamide Lawal ya yi kira na musamman ga shugabannin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa kan su hakura su janye.

Olamide Lawal ya yi kira ga Omoyele Sowore da sauran jagororin zanga zangar kan su bi hanyar sulhu da gwamnatin tarayya ta buƙata.

Ana zargin Sowore ya na cikin masu ba zanga-zangar goyon baya a kafafe duk da bai Najeriya.

Maganar Lawal kan sauraron Tinubu

Kwamared Olamide Lawal ya ce ya ji takaici kan yadda matasa masu zanga zanga suka bijirewa maganar shugaba Bola Tinubu kan tattaunawa.

Lawal ya ce neman tattaunawa da Bola Tinubu ya yi alama ce da ke nuna ya saurari yan kasa kuma zai biya bukatunsu.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Matasa sun nuna turjiya bayan an yi musu ruwan borkonon tsohuwa

Lawal: 'Mu kaucewa tarzoma a Najeriya'

Haka zalika Olamide Lawal ya bukaci yan Najeriya su saka fatan samun cigaban Najeriya a ransu a ko da yaushe maimakon yin abin da zai jawo tarzoma.

Ya ce lallai shugaba Tinubu ya dauko hanyar gyaran Najeriya da aka lalata a shekarun baya saboda haka yana buƙatar kawo goyon bayan al'umma.

Zanga zanga: Gumi ya yi kira ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ta shiga kwana ta shida inda aka rika samun canje canje kan yadda take gudana.

Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya kawo shawarar cewa a dawo tallafin man fetur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng