Ana Kuka da APC, Ganduje Ya Dafe Jiga Jigan PDP, Sun Daukarwa Jam'iyya Alkawari
- Yayin da ake cigaba da kushe tsarin mulkin APC a Najeriya, jamiyyar tana karbar sababbin tuba wadanda suka baro jam'iyyar PDP
- Tsohuwar shugabar matan jam'iyyar PDP da dubban magoya bayanta sun watsar da jam'iyyarsu inda suka shigo APC a jihar Ondo
- Mrs. Esther Ebieonjumi ta ba Gwamna Lucky Aiyedatiwa tabbacin kawo masa nasara a mazabar Ondo ta Kudu a zaben gwamna mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Ana daf da gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo, jiga-jigan jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC.
Tsohuwar shugabar matan jam'iyyar PDP, Mrs. Esther Ebieonjumi ta watsar da jam'iyyarta tare da tarewa da APC.
Ondo: Jiga-jigan PDP sun dawo jam'iyyar APC
Tribune ta tattaro cewa bayan ficewar Mrs. Esther, wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP da dama sun runtuma APC mai mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Esther ta ce ta koma APC ne saboda salon mulkin Gwamna Lucky Aiyedatiwa wanda ya kawo abubuwan cigaba a jihar.
Ta ce ta watsar da PDP ne saboda rashin shugabanci inda ta tabbatar da ficewarta ga gwamnan da sauran matan yankin Okitipupa, cewar Vanguard.
Har ila yau, Esther ta yiwa Gwamna Aiyedtiwa alkawarin kawo masa nasara a yankin Ondo ta Kudu a zaben da za a gudanar a watan Nuwamba.
Idan ba a manta ba, Mrs. Esther ta yi murabus ne daga mukaminta na shugabar matan PDP a watan da ta gabata, kafin dawowa APC.
Gwamna Aiyedatiwa ya ji dadin dawowarsu APC
A martaninsa, Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana zuwan Esther da magoya bayanta a matsayin cigaba ga APC a jihar baki daya.
Aiyedatiwa ya ba da tabbacin cewa mutane da yawa za su cigaba da shigowa APC ciki har da manyan shugabannin PDP.
Tutocin Rasha: Jigon APC ya shawarci Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa jigon jam'iyyar APC ya yi magana kan masu daga tutocin kasar Rasha inda ya shawarci Bola Tinubu kan haka.
Podar Johnson Yiljwan daga jihar Plateau ya shawarci Tinubu ya kira shugabannin masu zanga-zanga kan alakar tutuocin rasha a lamarin.
Jigon APC ya ce babu tsari kwata-kwata a zanga-zangar illa cigaba da takura al'umma da kuma kara tashin hankali a kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng