Bayan Gargaɗin Sojoji, An Dauki Matakin Doka Ta Hanyar Aika 'Yan Zanga Zanga Kurkuku
- Rundunar yan sanda a jihar Kaduna ta bayyana halin da ake ciki a jihar bayan an kama masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa
- Kakakin rundunar yan sanda a jihar Kaduna, SP Mansur Hassan ne ya bayyana halin da ake ciki ga manema labarai a jiya Litinin
- Haka zalika SP Mansur Hassan ya bayyana irin laifuffukan da masu zanga zangar suka aikata da matakin da aka dauka a kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Kaduna ta fitar da bayani kan masu zanga zanga da ta kama.
Rundunar ta bayyana cewa ta mika masu zanga zangar a gaban kotu kuma alkali ya yanke musu hukuncin da ya dace.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa kakakin yan sandan jihar ne, SP Mansur Hassan ya yi jawabin ga manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin da aka dauka kan masu zanga zanga
Rundunar yan sanda a jihar Kaduna ta bayyana cewa an gurfanar da masu zanga zangar da aka kama su 26 a kan tayar da tarzoma.
Haka zalika rundunar ta sanar da cewa an tura mutanen gidan gyaran hali bayan an kama su da laifi kuma ba su cika sharuddan beli ba.
An kama mutum 39 wajen zanga zanga
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta kama karin masu zanga zanga 39 bisa zargin aikata laifuffukan da suka hada da lalata dukiyar al'umma.
Dadin dadawa an same su da laifin ɗaga tutar kasar Rasha da ƙasar Sin a lokacin zanga zangar da aka yi a Kaduna.
Maganar kwamishinan yan sandan Kaduna
Kwamishinan yan sanda a Kaduna, CP Audu Idi Dabigi ya yi kira ga al'umma kan buƙatar cigaba da ba yan sanda hadin kai a wannan lokacin.
Arise News ta wallafa cewa rundunar ta tabbatar da kama tela da yake ɗinka tutar kasar Rasha, ta kama tutocin Rasha 38 da tutar Sin daya da sauransu.
'Yan zanga-zanga sun toshe hanya a Osun
A wani rahoton, kun ji cewa matasan Najeriya na cigaba da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya da aka fara tun ranar 1 ga watan Agusta.
Wasu matasa masu zanga zanga a jihar Osun da ke kudancin Najeriya sun fice daga wuraren da aka ware musu zuwa kan hanyoyin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng