Dattawan Arewa Sun Fadi Illolin da ba a Taba Samu a Yankinsu ba sai a Mulkin Tinubu
- A ranar Lahadi shugaban kasa Bola Tinubu ya yi jawabi ga yan kasa kan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da ake yi a Najeriya
- Kalaman da Bola Tinubu ya yi sun tayar da kura inda mutane da dama suka masa martani mai zafi daga sassa daban daban
- Dattawan Arewa sun yi martani mai zafi ga Bola Tinubu kan cewa jawabin da ya yi bai dauko hanyar kawo gyara a Arewa ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar dattawan Arewa ta yi martani ga Bola Tinubu kan jawabin da ya yi bayan fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.
A ranar Lahadi ne shugaban kasar ya yi jawabi ga yan Najeriya kan halin da ake ciki da manufofin gwamnatinsa.
Jaridar Punch ta wallafa cewa sakataren kungiyar dattawan Arewa, Abdulaziz Sulaiman ne ya fitar da sanarwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsalar da Bola Tinubu ya kawo Arewa
Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta ce mulkin Bola Tinubu ya kara ruruta matsalar tsaro da ta jawo yan gudun hijira marasa adadi a yankin.
NEF ta ce hakan ya kara kawo matsalolin yawaitar miliyoyin marayu da aka kashe iyayensu suke fama da yunwa mai tsanani.
Premium Times ta wallafa cewa kungiyar dattawan ta ce ba a taba samun haka a tarihin Arewacin Najeriya ba sai a mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
NEF: 'Jawabin Tinubu bai cika ba'
Kungiyar dattawan Arewa ta ce jawabin da Bola Tinubu ya yi ya bar giɓi mai girma a harkar tsaro a jihohin Arewacin Najeriya.
Kungiyar ta ce bai kamata shugaban ya kammala zance ba tare da yin bayani kan yadda zai magance matsalolin tsaron Arewa ta yamma ba.
A ƙarshe, kungiyar ta yi kira na musamman ga Bola Tinubu kan mayar da hankali a kan abin da ya shafi tsaro da walwalar mutanen Arewa.
An yi martani ga jawabin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya inda ya amince da koke-kokensu tare da bayyana shirye-shiryen gwamnatinsa.
‘Yan Najeriya sun mayar da martani kan jawabin Tinubu a shafukan sada zumunta, inda wasu ke nuna goyon baya yayin da wasu ke sukar shugaban.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng