“Komai Ya Kare”: 'Yan Kano Sun Fadi Illar da Zanga Zanga Ta Yi Musu Game da Abinci

“Komai Ya Kare”: 'Yan Kano Sun Fadi Illar da Zanga Zanga Ta Yi Musu Game da Abinci

  • Zanga-zangar da ake cigaba da yi ta fara yin illa ga wasu musamman mazauna Kano yayin da aka shiga rana ta shida
  • Wasu mazuna Kano sun koka kan yadda suke neman kayan masarufi da suka hada da sukari da fulawa tsawon kwanaki
  • Hakan bai rasa nasaba da cigaba da zanga-zanga da ake yi a fadin Najeriya kan halin kunci da ake ciki na tsadar rayuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Mazauna Kano da dama sun fara kokawa kan yadda aka fara rasa kayan masarufi dalilin zanga-zanga da ake yi.

Hakan bai rasa nasaba da cigaba da zanga-zanga da ake yi da kasuwanni suka kasance a kulle na tsawon kwanaki.

Kara karanta wannan

Sojoji sun karbi mulki yayin da zanga zanga ta tsananta a Bangladesh, an samu bayanai

Mazauna Kano sun kosa da cigaba da zanga-zanga
Mazauna Kano sun fadi halin da suke ciki na rashin kayan masarufi saboda zanga-zanga. Hoto: @babarh.
Asali: Twitter

Kano: Karancin kayan masarufi saboda zanga-zanga

Daily Trust ta tattaro cewa an fara samun karancin sukari da fulawa da sauran kayayyakin abinci da ake amfani da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mai shago da ake kira Gambo Muhammad a Nassarawa ya ce dole ya kulle shagonsa saboda kayan sun kare a ciki.

Ya ce ya kulle shagon ne ba wai domin tsoron sata ba sai dai saboda rashin kaya a ciki bayan kasuwanni sun kasance a kulle.

Mazaunin Kano ya koka da zanga-zanga

Sai kuma Bashir Bello daga Sharada ya ce suna cikin wani hali inda ya ce ya kwashe kwanaki biyu yana neman sukari da fulawa amma bai samu ba.

Ya ce a yanzu samun wasu kayayyaki musamman na abinci sun yi karanci saboda rashin kasuwanci dalilin zanga-zanga.

Bincike ya tabbatar da cewa a yanzu kayan masarufi sun fara tashi saboda rashin wadatar kayan a shaguna da kasuwanni.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

Zanga-zanga: Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta yi magana kan abubuwan da suka faru a sakamakon zanga-zangar adawa da gwamnatin Bola Tinubu da ake yi a fadin kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe matasa da dama a Kano yayin da a hannu daya kuma 'yan daba suka fasa shagunan jama'a tare da sace kayayyaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.