Babban Hafsan Tsaro Ya Fadi Laifin Masu Daga Tutar Rasha, Ya Gargadi 'Yan Zanga Zanga
- Babban hafsan haafsoshin tsaro ya yi magana kan masu ɗaga tutar Rasha yayin zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan
- Janar Christopher Musa ya bayyana ɗaga tutar wata ƙasa babban laifi ne na cin amanar ƙasa kuma ko kaɗan ba za su amince da hakan ba
- Ya ja kunnen masu kiran da a yi juyin mulki inda ya bayyana cewa sun gamsu da mulkin dimokuraɗiyya kuma ba za su kifar da gwamnati ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Mustapha, ya ce waɗandaa ke ɗaga tutar Rasha a Najeriya sun aikata laifin cin amanar kasa.
Janar Christopher Musa ya bayyana hakan ne bayan kammala wani taron gaggawa na tsaro da Shugaba Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.
Hafsan hafsoshin tsaron ya sha alwashin cewa doka za ta yi aikin a kan irin waɗannan mutanen, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane gargaɗi hafsan tsaro ya yi?
Babban hafsan tsaron ya gargaɗi masu kiran da a yi juyin mulki, inda ya bayyana cewa sojoji sun amince da mulkin dimokuraɗiyya kuma ba za su taɓa bari a kifar da gwamnati ba.
"Mun ga yadda ake ɗaga tutocin ƙasashen waje a Najeriya, wannan bai dace ba. Muna gargaɗi kuma shugaban ƙasa ya ce mu faɗi cewa ba za mu amince wani ya riƙa ɗaga tutar wata ƙasa a Najeriya ba.
"Wannan laifin cin amanar ƙasa ne kuma za mu ɗauki mataki a kan hakan. Saboda haka kada wanda ya bari wani ya yi amfani da shi."
"Da yawa daga cikin masu ɗaga tutocin, yara ne waɗanda ake sanyawa su yi hakan. Muna bibiyar waɗanda ke ɗaukar nauyinsu, kuma za mu ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kan hakan.
"Mun faɗi cewa sojoji ba za su bari abubuwa su dagule ba, ga shi yanzu a bayyane wasu na sanyawa ana ɗaga tutar Rasha a Najeriya, wannan keta iyaka ne kuma ba zamu amince da hakan ba."
- Janar Christopher Musa
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Zanga zanga: An kama mutumin da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano
- Kasar Rasha ta yi magana kan masu zanga zangar da ke ɗaga tutocinta a Najeriya
- Legas: 'Yan daba sun kai mamaya kusa da ofishin gwamna, an tarwatsa masu zanga zanga
Jami'an tsaro sun cafke masu zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar da suka fito ranar Litinin, 5 ga watan Agustan 2024 a birnin tarayya Abuja.
Masu zanga-zangar sun fito ne a yankin Karu na birnin Abuja domin ci gaba da nuna adawa kan halin ƙuncin da ake fama da shi a ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng