"Ba Tinubu ba ne": Jigo a PDP Ya Fadi Mai Laifi Kan Halin da Najeriya ke Ciki

"Ba Tinubu ba ne": Jigo a PDP Ya Fadi Mai Laifi Kan Halin da Najeriya ke Ciki

  • Sanata Nicholas Tofowomo ga fito ya bayyana cewa bai kamata a ɗora alhakin halin da ƙasar nan ke ciki ba kan Shugaba Bola Tinubu
  • Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa ba Tinubu ba ne ya cire tallafin man fetur a ƙasar nan, shi kawai sanar da cirewan ya yi
  • Ya yi nuni da cewa gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ce ta cire tallafin man fetur ɗin da talaka ke amfana da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Jigo a jam’iyyar PDP a jihar Ondo, Nicholas Tofowomo, ya ce bai kamata a ɗora laifin halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan kacokan kan Shugaba Bola Tinubu ba.

Nicholas Tofowomo ya bayyana cewa halin taɓarɓarwar da tattalin arziƙin ƙasar nan ke ciki ba laifin shugaban ƙasan ba ne.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Abin da Tinubu ya faɗawa hafsoshin tsaro kan masu ɗaga tutar Rasha

Jigon PDP ya goyi bayan Tinubu
Jigon PDP ya kare Tinubu kan halin da kasar nan ke ciki Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jigon na PDP wanda ya wakilci mazabar Ondo ta Kudu a majalisar dattawa ta tara, ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Okitipupa, cewar rahoton jaridar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon PDP ya kare Bola Tinubu

Tsohon sanatan ya bayyana cewa bai kamata a ɗorawa Shugaba Tinubu alhakin matsalolin da ƙasar nan ta samu kanta a ciki ba, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Sai dai, ya yi nuni da cewa cire tallafin man fetur da wasu manufofin gwamnatin Tinubu kan tattalin arziƙi sun ƙara rura wutar lalacewar abubuwa a ƙasar nan.

'Dan siyasar ya yi nuni da cewa gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta cire tanadin tallafin man fetur a kasafin kuɗin 2023.

"Tinubu gadar matsalar ya yi" - Sanata Nicholas

Tsohon Sanatan ya ci gaba da cewa, Tinubu wanda ya gaji kasafin kudin ne kawai ya bayyanawa ya yi tare da ɗaukar nauyin cire tallafin.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: An kama mutumin da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano

"Ina cikin ƴan majalisar dattawa ta tara da ta amince da kasafin kuɗin 2023. Babu tanadin biyan tallafin man fetur a cikin kasafin kuɗin. Saboda haka gwamnatin Buhari ce ta cire tallafin man fetur."
"Maganar gaskiya Tinubu ya gaji kasafin kuɗin ne kawai sannan ya sanar da cire tallafin a lokacin jawabinsa na farko a ranar 29 ga Mayu, 2023, kuma ya ɗauki alhakin hakan."
"Saboda haka ina tunanin bai kamata mu ɗora masa laifi ba kan halin da da ake fama da shi a ƙasar nan yanzu ba."

- Sanata Nicholas Tofowomo

Karanta wasu labaran kan gwamnatin Tinubu

Ministan Buhari ya yi wa Tinubu martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan matasa da bunƙasa harkokin wasanni, Solomon Dalung ya caccaki jawabin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kan zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Janar Ibrahim Babangida na son sojoji su kwace mulki? Gaskiya ta fito daga bakin IBB

Dalung, wanda ya riƙe kujerar minista a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ce jawabin Shugaba Tinubu ba zai tsaida zanga-zanga ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng