Kaduna, Zariya: Gwamna ya Sanya Dokar Hana Fita ta Awa 24, An ba Jami’an Tsaro Umarni

Kaduna, Zariya: Gwamna ya Sanya Dokar Hana Fita ta Awa 24, An ba Jami’an Tsaro Umarni

  • Gwamnatin Kaduna ta samu kwararan hujjoji da suka tabbatar da cewa wasu miyagu sun kwace zanga-zangar da ake yi a jihar
  • Da wannan, gwamnatin ta sanar da sanya dokar hana fita ta awanni 24 a garuruwan Kaduna, Zariya da kewaye tare da gargadar jama'a
  • Da muka zanta da Abubakar Ismail, wani matashi wanda ya fita zanga-zangar a Kaduna ya ce yana fargabar sanarwar ta zo a kurarren lokaci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Majalisar tsaro ta Kaduna ta yanke shawarar sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a garuruwan Kaduna da Zariya da ke jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da aka ruwaito cewa masu zanga-zanga sun koma fasa shaguna, gidaje tare da sace kayan jama'a da na gwamnati.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnatin Kano ta ɗauki matakai 6, ta yi magana kan ɗaga tutar Rasha

Gwamna Uba Sani ya sanya dokar hana fita a Kaduna da Zariya.
Kaduna: Gwamnati ta sanya dokar hana fita ta awa 24 saboda zanga-zanga. Hoto: @samuelaruwan
Asali: Twitter

Gwamnatin Kaduna ta fitar da sanarwa

Samuel Aruwan, kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna ya sanar da hakan a shafinsa na X a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Aruwan ya ce majalisar tsaron ta dauki wannan matakin ne bayan gabatar da rahoton halin tsaro da jihar take ciki ga Gwamna Uba Sani.

Sanarwar ta yi ikirarin cewa gwamnatin jihar ta gano wasu bata gari sun kwace zanga-zangar lumanar inda suka rikidar da ita zuwa satar kayan jama'a.

Zanga-zanga: Gwamnatin Kaduna ta dauki matakai

Majalisar tsaro ta jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, bayan ta yi nazari a kan harkokin tsaro a jihar, ta dauki matakai hudu kamar haka:

1. 'Yan daba sun kwace zanga-zangar Kaduna

Gwamnatin ta ce akwai isassun hujjoji da ke nuna karara cewa wasu miyagu nsun kwace zanga-zangar da ake ci gaba da yi, inda suka koma fasa shaguna da lalata dukiyoyin gwamnati da na jama’a.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga na daga tutar Rasha a Kaduna, an fara awon gaba da kayan jama'a

2. An sanya dokar hana fita ta awa 24

Dangane da wannan abin takaici, majalisar tsaro ta jihar Kaduna ta yanke shawarar kafa dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a garuruwan Kaduna da Zariya da kewaye ba tare da bata lokaci ba.

3. An yi kira ga mazauna jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta shawarci 'yan jihar da su kasance a cikin gida yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da kokarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

4. Gwamnatin Uba za ta rika duba dokar

Sanarwar Mista Aruwan ta kuma ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da sa ido domin duba dokar hana fitar idan har bukatar hakan ta taso.

Za mu bi umarnin gwamnati - Matashi

A zantawarmu da wani matashi Abubakar Ismail wanda ya fita zanga-zanga a kan titin Nnamdi Azikwe da ke Igabi, Kaduna, ya ce za su bi umarnin gwamnatin jihar na zaman gida.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta ci shugabar kasa, Firayim Minista ta tsere da aka zagaye fadar ta

Sai dai Abubakar ya ce wannan umarnin ya zo a ne a kurarren lokaci la'akari da cewa tuni matasa suka fantsama a cikin garin domin gudanar da zanga zanga.

"Ina fargabar cewa jami'an tsaro na iya daukar mataki kan matasan a lokacin da suke kokarin komawa gida, alhalin an ba da dokar a kurarren lokaci.
"Kamata ya yi ace an bayar da wannan dokar tun a daren ranar Lahadi, ka ga babu wanda zai fito ya yi zanga zanga yau Litinin."

Masu zanga-zanga na daga tutar Rasha

A wani labarin, mun ruwaito cewa masu zanga-zanga a jihar Kaduna sun mamaye manyan tituna yayin da suke daga tutar kasar Rasha duk a cikin adawa da tsadar rayuwa.

An ruwaito cewa, masu zanga-zangar sun fasa gidajen jama'a da wasu kadarori na gwamnati inda suka rika satar kayayyaki a yankin titin NEPA da ke kwaryar jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.