Jami'an Tsaro Sun Cafke Masu Zanga Zangar Lumana a Abuja

Jami'an Tsaro Sun Cafke Masu Zanga Zangar Lumana a Abuja

  • Jami'an tsaro sun dasa wawa kan wasu masu zanga-zanga da suka fito a birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 5 ga watan Agustan 2024
  • Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya bayyana cewa jami'an tsaron sun harba musu barkonon tsohuwa domin tarwatsa su sannan suka cafke mutum uku
  • Hakan na zuwa ne yayin da matasa ke ci gaba da fitowa kan tituna a faɗin ƙasar nan domin nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki duk da kiran da Bola Tinubu ya yi na a dakata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar da suka fito ranar Litinin a birnin tarayya Abuja.

Masu zanga-zangar sun fito ne a yankin Karu na birnin Abuja domin ci gaba da nuna adawa kan halin ƙuncin da ake fama da shi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Rana ta 3: Jami'an tsaro sun cafke 'yan jarida da masu zanga-zanga

Jami'an tsaro sun cafke masu zanga-zanga a Abuja
Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga

Jaridar The Punch ta rahoto cewa masu zanga-zangar sun fara taruwa ne lokacin da jami'an tsaron suka dira a kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaron bayan sun rufarwa masu zanga-zangar sun cafke mutum uku daga cikinsu, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Da yake magana da manema labarai, ɗaya daga cikin masu zanga-zangar mai suna, Yahaya Abdullahi, ya bayyana cewa jami'an tsaron sun harba musu barkonon tsohuwa.

"Mutanenmu sun fara fitowa ne kawai sai ƴan sanda da sauran jami'an tsaro suka fara harba mana barkonon tsohuwa sannan suka cafke wasu daga cikinmu. Ya zuwa yanzu mun san mutum uku da aka kama."

- Yahaya Abdullahi

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun yi ta harbin masu zanga zanga a Abuja, an yi barna

Jami'an DSS sun cafke jagoran zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun cafke daya daga cikin manyan jagororin masu zanga-zangar adawa da halin ƙunci a babban birnin tarayya Abuja.

Jami'an na hukumar DSS sun cafke jagoran mai suna Micheal Lenin da misalin ƙarfe 2:00 na daren ranar Litinin a gidansa da ke Apo a birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng