Babbar Kungiyar Yarbawa Ta Juya Baya Ga Tinubu, Ta Masa Zazzafan Martani

Babbar Kungiyar Yarbawa Ta Juya Baya Ga Tinubu, Ta Masa Zazzafan Martani

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na cigaba da shan suka kan kalaman da ya yi a ranar Lahadi game da masu zanga zanga
  • Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta yi Allah wadai da kalaman da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi kan masu zanga zangar
  • Afenifere ta ce maganar cewa akwai siyasa a cikin zancen zanga zanga da gwamnatin tarayya ta yi ba gaskiya ba ne kwata kwata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta yi martani mai zafi ga shugaba Bola Tinubu kan maganganun da ya yi ranar Lahadi.

Shugaba Bola Tinubu ya yi magana ne kan zanga zangar tsadar rayuwa da matasa suka fara tun ranar 1 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Wole Soyinka ya fadi kuskuren Tinubu bayan jawabinsa kan zanga zanga

Bola Tinubu
Kungiyar Yarabawa ta bukaci Tinubu ya dawo da tallafi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kungiyar Afenifere ta ce akwai bukatar shugaba Bola Tinubu ya saurari masu zanga zangar yadda ya kamata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Afenifere: 'Cire tallafi ba zai yiwu ba'

Jaridar 21st Century Chronicle ta wallafa cewa kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta ce akwai bukatar Bola Tinubu ya sake lura da maganar dawo da tallafin man fetur.

Afenifere ta ce cire tallafi da sauran tsare tsaren tattalin arzikin zamani sun gaza aiki a kasashe da dama a fadin duniya saboda haka bai kamata Najeriya ta bi tsarin ba.

Ba maganar sulhu da matasa inji Afenifere

Sakataren yada labaran Afenifere, Justice Fakiyesi ya ce maganar zama da masu zanga zanga da Bola Tinubu ya fada ba ta ta so ba.

Justice Fakiyesi ya ce abin da ya kamata kawai shi ne canza tsare tsaren da gwamnatin Bola Tinubu ta kawo domin saukaka rayuwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

Akwai siyasa a cikin zanga zanga?

Haka zalika kungiyar Afenifere ta ce ba maganar siyasa a cikin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da aka fara a Najeriya kamar yadda shugaban kasa ya fada.

Ta ce kamar yadda Tinubu ya yi zanga zanga a lokacin shugaba Goodluck Jonathan haka shi ma dole ya yi hakuri da abin da ya gani.

Yan Najeriya sun yi martani ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya inda ya amince da koke-kokensu tare da bayyana shirye-shiryen gwamnatinsa.

Yan Najeriya sun mayar da martani kan jawabin Tinubu a shafukan sada zumunta, inda wasu suka nuna goyon baya yayin da wasu suka soki shugaban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng