Rana ta 5: Duk da Barazanar 'Yan Daba, Masu Zanga Zanga Sun Sake Fitowa
- Masu gudanar da zanga-zanga a jihar Legas sun nuna jarumta bayan sake fitowa filin Ojota bayan 'yan daba sun fatattakesu
- 'Yan daba sun kori masu gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a ranar Lahadi
- Wasu masu zanga-zangar sun bayyana cewa ba za su daina fitowa ba har sai Tinubu da dauki makan share masu hawaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Legas - Wasu 'yan Najeriya sun sake fitowa filin Freedom Park da ke Ojota a jihar Legas duk da tarwatsa taronsu da 'yan daba su ka yi ranar Lahadi.
Wasu daga cikin jagororin kungiyoyin da ke gudanar da zanga-zanga sun bayyana janyewarsu bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabin neman tattaunawa.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa amma wasu kungiyoyin matasa, na Socialist Workers League da Democratic Social Movement sun ce za su ci gaba da neman hakkinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Za mu cigaba da fitowa zanga-zanga," Matasa
Matasa a jihar Legas sun fito ci gaba da zanga-zangar lumana a jihar duk da lamarin ya rikide zuwa rikici a wasu jihohin, wasu kuma 'yan daba su ka koresu.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa an samu 'yar hatsaniya tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaron da su ka dauke motar daya daga cikinsu.
Wata Precious Oruche da ta fito zanga-zangar ta ce za su ci gaba da neman hakkinsu, domin ko kadan shugaban kasa bai duba matsalolin kasar nan ba.
An kafa kwamitin kan kisan masu zanga-zanga
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta samar da kwamitin da zai yi bincike a kan kisan mutane da dama da suka fito zanga-zanga a wasu daga cikin unguwannin Kano.
Daga cikin wasu ayyukan da kwamitin zai yi akwai binciken wasu da ake zargin 'yan daban haya ne su ka rika kwace kayan jama'a da sace wadansu a sassa daban-daban na jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng