Jawabin Tinubu Ya Bar Baya da Ƙura, Manya Sun Zargi Shugaban Ƙasa da Rashin Tausayi
- Jawabin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ga masu zanga-zanga bai gamsar da jama'a ba domin babu abin da ya shafi kokensu
- Daga cikin wadanda ke ganin babu wani abin a zo a gani da jawabin shugaban akwai Atiku Abubakar da fitaccen lauya Femi Falana
- Tsohon mataimakin shugaban kasan da wasu jagorori na ganin jawabin shugaban bai bayyana kudirin rage radadin da ake ji ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Tun bayan jawabin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ga 'yan kasar nan ga masu zanga-zanga aka samu wadanda su ka caccaki furucin.
Wasu daga cikin jagorori a kasar na ganin jawabin bai yi kusa da ƙoƙarin magance koken da ya sabbaba zanga-zangar gama gari ba.
Daily Trust ta wallafa cewa wadanda su ka caccaki jawabin shugaban kasar na ganin ba a dauko hanyar magance matsalolin 'yan kasar nan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin Tinubu: Me shugabanni su ka ce?
Daga cikin jagorori a kasar nan da su ka ga rashin dacewar jawabin shugaban kasar akwai Atiku Abubakar, fitaccen marubuci, Wole Soyinka, shararren lauya Femi Falana da sauran kungiyoyi.
1. "Tinubu ya gaza share hawayen 'yan kasa," Atiku
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar na ganin babu wani abin da Tinubu ya fadi da ke da dangantaka da koken 'yan kasa.
Ya ce an yi zaton shugaban zai bayyana wasu manya-manyan kudurori da za su rage radadin da 'yan kasa ke fuskanta, Punch ta wallafa.
2. "A magance matsalar kasa," Falana ga Tinubu
Fitaccen lauya, Femi Falana SAN na ganin da shugaban ya yi jawabin kai tsaye ga masu zanga-zanga da magana a kan matsalolinsu, za su duba yiwuwar janye zanga-zanga.
Falana ya kara da nuna muhimmancin gwamnati ta yi kokarin magance rashawa a tsakanin wadanda ke bangaren man fetur.
3. "Bai kamata a harbi matasa ba," Soyinka
A furucinsa a karon farko bayan Tinubu ya dare mulkin kasar nan, Wole Soyinka ya yi jawabi saboda harbin jama'a a zanga-zanga.
Ya bayyana cewa wannan ba lokacin harba harsashi tsakanin matasan da yunwa ta yiwa katutu ba ne, inda ya ce hakan zai kara jawo tashe-tashen hankula.
An kori masu zanga-zanga bayan jawabin Tinubu
A wani labarin kun cewa wasu 'yan daba sun fatattaki masu zanga-zanga a jihar Legas bayan jawabin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ga 'yan kasa.
'Yan daban na ganin babu dalilin da jama'a za su fito tituna domin nuna adawa ga manufofin gwamnati tun da har shugaban da kansa ya yi masu jawabi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng