Ana Cikin Zanga Zangar Lumana an Jefa Filato Cikin Matsala

Ana Cikin Zanga Zangar Lumana an Jefa Filato Cikin Matsala

  • A yayin da ake zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya an samu matsaloli a jihohi da dama a Arewacin Najeriya
  • Matasa sun fara zanga zanga lafiya a jihar Filato na kwanaki hudu kafin a jefa su cikin matsala da ta jawo a aka rufe sassan jihar
  • An samu rahotanni na dawowar kwanciyar hankali a wasu jihohi bayan samun tashin hankali yayin zanga zangar tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Matsala ta shigo cikin zanga zanga a jihar Filato bayan fara gudanar da ita lami lafiya.

Musulmai da Kiristoci sun kasance suna zanga zangar tsadar rayuwa lami lafiya kafin samun matsalar a birnin Jos.

Kara karanta wannan

Yadda yan sanda suka hallaka Bayin Allah lokacin zanga zanga a jihar Kano

Zanga zanga
Matasa sun yi barazana ga yan kasuwa a Filato. Hoto: Anas Yunus
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an fara samun kwanciyar hankula a wasu jihohin Najeriya bayan an shiga firgici saboda zanga zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Filato: Yadda aka fara zanga zanga

An fara zanga zangar a birnin Jos lami lafiya kuma an samu hadin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci.

An ruwaito cewa Musulmai sun yi sallar Juma'a a filin zanga zangar haka zalika Kiristoci sun yi ibada ranar Lahadi a wajen zanga zangar.

Matsalar da ta kunno kai a Filato

Bayan shafe kwanaki hudu ana zanga zangar lumana an samu wasu matasa da suka fara shirin satar kayan mutane.

Matasan sun tura saƙon barazana ga masu shaguna kan cewa za su kwashe musu kaya ko su fito zanga zanga a ranar Litinin wanda hakan yasa kafa dokar taƙaita zirga zirga a jihar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Matasa sun nuna turjiya bayan an yi musu ruwan borkonon tsohuwa

Jama'a sun soki wannan musamman ganin ana kokarin yaki ne da zaluncin masu mulki.

An samu zaman lafiya a jihohi

Bayan samun tashin hankali a jihar Gombe a lokacin zanga zangar, an ruwaito cewa an cigaba da gudanar da ayyuka bayan hankula sun kwanta.

Haka zalika an ruwaito cewa an samu zaman lafiya a jihar Jigawa bayan an janye dokar taƙaita zirga zirga a jihar saboda tashin hankali da aka samu.

Kano: An kashe masu zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa an samu sabani da jami'an tsaro musamman yan sanda da masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin Najeriya.

A jihar Kano, an samu rikici tsakanin matasa da yan sanda a unguwannin Kurna da Nasarawa wanda hakan ja jawo asarar rayuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng