DSS ta Fara Daukar Mataki kan Masu Shirya Zanga Zanga a Abuja, an Cafke Jagoransu
- Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar DSS sun shiga har gidan wani jagoran masu zanga-zanga a Abuja sun yi awon gaba da shi
- An ce jami'an sun kutsa gidan Micheal Lenin da misalin karfe 2 na daren ranar Litinin a unguwar Apo inda suka fara cin zarafinsa kafin kama shi
- Bisa ga abubuwan da suka faru a jiya Lahadi, ana zargin an kama Lenin ne bayan ya nemi a ci gaba da zanga-zanga bayan jawabin Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jami'an hukumar tsaro ta DSS sun cafke daya daga cikin manyan jagororin masu zanga-zangar 'adawa da mummunar gwamnati' a babban birnin tarayya Abuja.
An ce jami'an DSS sun cafke jagoran mai suna Micheal Lenin da misalin karfe 2 na daren ranar Litinin a gidansa da ke Apo a birnin Abuja.
Da yake magana da jaridar The Punch, daraktan gangamin 'Take It Back,' Damilare Adenola, ya ce jami'an DSS sun yiwa gidan Lenin kawayanya kafin suka kama shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DSS sun cafke jagoran masu zanga-zanga
Damilare Adenola ya yi ikirarin cewa sai da jami'an tsaron suka ci zarafin Lenin kafin suka tafi da shi.
A cewar Adenola:
"Hukumar DSS ta kama Lenin. An dauke shi ne a wani samame da aka kai gidansa da misalin karfe biyu na dare.
“An kama shi tare da azabtar da shi a gaban iyalinsa. Muna neman gaggauta sakinsa ba tare da wani sharadi ba.”
Ba a samu damar jin ta bakin mai magana da yawun hukumar ta DSS, Peter Afunanya ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Lenin ya yi martani ga jawabin Tinubu
Har yanzu bai amsa sakon da aka aika masa ba, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.
Lenin na daya daga cikin wadanda suka shirya taron manema labarai inda suka nuna rashin jin dadinsu da jawabin Shugaba Bola Tinubu a ranar Lahadi.
A jawabin da ya yi, ya ce jawabin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ya nuna cewa bai damu da halin da ake ciki a kasar ba.
Hakazalika, Lenin ya ce za a ci gaba da gudanar da zanga-zangar ne a ranar Litinin, inda ya yi kira ga ‘yan kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu.
DSS sun kama jagororin masu zanga-zanga
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu shugabannin da suka jagoranci zanga-zangar nuna adawa da halin ƙunci da rashin tsaro a jihar Katsina sun faɗa hannun hukumar DSS.
Kabir Shehu Yandaki da Habibu Ruma, shugabannin zanga-zangar "Struggle for Good Governance" an gayyace su zuwa ofishin DSS da ke Katsina, inda daga bisani aka tsare su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng