Attajirin Afrika Ta Kudu Ya Zama Mafi Arziki a Nahiya, Dangote Ya Samu Sabon Matsayi

Attajirin Afrika Ta Kudu Ya Zama Mafi Arziki a Nahiya, Dangote Ya Samu Sabon Matsayi

  • Attajirin da ya fi kowa kudi a Najeriya, Aliko Dangote, ya sauko kasa a jerin masu kudin Afrika a sabon rahoton da aka fitar a Agustan
  • Dangote ya koma matsayi na biyu bayan hamshakin attajirin Afrika ta Kudu Johann Rupert, shugaban Compagnie Financière Richemont
  • A cikin shekaru 10 da suka wuce, dan kasuwa mafi arziki a Najeriya, Dangote, shi ne ya rike mukamin attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Attajirin kasar Afrika ta Kudu, Johann Rupert yanzu ya zama hamshakin mai kudin Afrika, inda ya zarce attajirin Najeriya, Aliko Dangote.

Rahotanni sun bayyana cewa arzikin Rupert ya karu zuwa dala biliyan 13.65, wanda ya sa ya koma na 154 a jerin masu kudin duniya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan yiwuwar dawo da tallafin mai a jawabinsa, bayanai sun fito

Johann Rupert ya shiga gaban Aliko Dangote a jerin masu kudin Afrika
Dangote ya rasa matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka a hannun Rupert. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoto ya ce an sha gaban Dangote

Mujallar Bloomberg ta rahoto cewa yanzu Rupert ya kere arzikin Dangote da tserayar dala miliyan 50, yayin da shi dangote ke da arzikin da ya kai dala biliyan 13.6 a ranar Juma'a, 2 ga Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sabon rahoton da Bloomberg ta fitar na attajiran duniya, Aliko Dangote ya rikito zuwa na 156 inda yake bin bayan Rupert na kasar Afrika ta Kudu.

Arzikin Aliko Dangote da Johann Rupert

Tun da shekarar 2024 ta fara, Dangote da Rupert sun ga canji sosai a yayin samun kudadensu da kuma taruwar arzikinsu.

Yayin da arzikin Rupert ya karu da dala biliyan 1.21 daga Janairu zuwa Agusta, karyewar darajar Naira ta jawo arzikin Dangote ya ragu sosai.

Mujallar Billionares.Africa ta bayyana cewa a cikin watanni shida, Dangote ya tafka asarar dala biliyan 10

Kara karanta wannan

Dalilin shigata zanga zangar lumana a Kano Inji tsoho mai shekaru kusan 70 a suniya

An ce Dangote ya samu arzikinsa ne daga hannun jarin kaso 86 da yake da shi a kamfanin simintin Dangote, kuma arzikinsa ya ta'allaka ga yanayin tattalin arzikin Najeriya.

Amma a hannu daya, an ce Rupert ya samu arzikinsa ne daga kamfaninsa na Cie Financière Richemont, wanda ke hada-hadar kayan alatu kuma shi ne kamfanin da ke kera agogo mafi tsada a duniya.

Ga jerin attajirai 10 mafi kudi a duniya

  1. Elon Musk: $241bn
  2. Jeff Bezos: $207bn
  3. Bernard Arnault: $182bn
  4. Mark Zuckerberg: $177bn
  5. Bill Gates: $157bn
  6. Larry Page: $153bn
  7. Larry Ellison: $152bn
  8. Steve Ballmer: $145bn
  9. Sergey Brin: $144bn
  10. Warren Buffett: $136bn

Adenuga ya doke BUA, ya dawo bayan Dangote

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mista Mike Adenuga ya dawo matsayinsa a rukunin attajiran Najeriya, ya tabbata a matsayin na biyu a kasar nan.

Mujallar Forbes ta fitar da jerin masu kudi a shekarar nan ta 2024, Mike Adenuga yana gaban Alhaji Abdul Samad Rabiu yayin da Aliko Dangote ke rike da kambun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.