Yadda Yan Sanda Suka Hallaka Bayin Allah Lokacin Zanga Zanga a Jihar Kano

Yadda Yan Sanda Suka Hallaka Bayin Allah Lokacin Zanga Zanga a Jihar Kano

  • An samu sabani da jami'an tsaro musamman yan sanda da masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin Najeriya
  • A Kano, an samu rikici tsakanin matasa da yan sanda a unguwannin Kurna da Rijiyar Lemu wanda hakan ja jawo asarar rayuka
  • Shahararren dan jarida daga jihar, Jafar Jafar ya yi magana kan mutanen da suka mutu a sanadiyyar zargin bude musu wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Yayin da ake cigaba da zanga zangar adawa da gwamnatin tarayya a kan tsadar rayuwa an samu mace mace a Kano.

Ana zargin cewa yan sanda ne suka bude wuta ga masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a unguwannin Kurna da Nasarawa.

Kara karanta wannan

Ana cikin zanga zangar lumana an jefa Filato cikin matsala

Zanga zanga
An kashe masu zanga zanga a Kano. Hoto: Jafar Jafar
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan wadanda aka kashe ne cikin wani sako da shahararren dan jarida, Jafar Jafar ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai kan wadanda aka kashe a Kano

Bayan labarai sun cika kafafen sada zumunta a kan cewa an kashe mutane da dama a lokacin zanga zanga a Kano, al'umma sun fara neman sahihan labarai kan lamarin.

Jafar Jafar ya tallata a shafinsa na Facebook cewa yana neman sahihan bayanai kan wadanda aka kashe yayin zanga zangar a Kurna da Nasarawa.

Zanga zanga: An kashe yara da mata a Kano

Biyo bayan tambayar da Jafar Jafar ya yi, ya wallafa cewa ya samu bayanai kan yadda aka kashe mutane ciki har da mata da yara kanana a unguwannin Kurna da Nasarawa.

Daɗin dadawa, Jafar Jafar ya wallafa a Facebook cewa an harbi wani karamin yaro da aka harba da harsashi yana zaune cikin gidansu, an yi sa yaron bai mutu ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan sandan Kano sun tashi tsaye, an fara bin gida gida neman kayan sata

Ana zargin cewa mutanen sun fito zanga zanga ne yayin da aka saka dokar taƙaita zirga zirga a jihar Kano.

An yi kira ga yan sanda a Kano

Bayan wallafa labarin, jama'a sun yi kira ga hukumomi da ayi bincike tare da hukunta yan sandan da suka aikata kisan.

Ana ganin cewa hukunta jami'an tsaron ne kawai zai saka a samu sauki wajen magance irin wadannan matsalolin a Najeriya.

CUPP ta yi magana kan zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da matasa ke cigaba da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya, kungiyar CUPP ta magantu.

Kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa ta CUPP ta bayyana babban kuskuren da gwamnatin Bola Tinubu ta yi a kan zanga zangar da aka fara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng