Janar Ibrahim Babangida Na Son Sojoji Su Kwace Mulki? Gaskiya Ta Fito Daga Bakin IBB

Janar Ibrahim Babangida Na Son Sojoji Su Kwace Mulki? Gaskiya Ta Fito Daga Bakin IBB

  • Tsohon shugaban ƙasa a zamanin mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya nesanta kansa da wani rubutu da aka danganta shi da shi
  • Janar IBB ya ce ko kaɗan rubutun wanda aka yi a shafin X mai cewa ya fi son mulkin soja a ƙasar nan fiye da na dimokuraɗiyya, ba daga gare shi ba ne
  • Tsohon shugaban ƙasan na Najeriya ya koka kan yadda shafin ya daɗe yana yaɗa kalaman ƙarya da sunansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ƙaryata batun cewa yana goyon bayan mulkin soja fiye da na dimokuraɗiyya.

Wani shafi ne dai ya danganta kalaman ga tsohon shugaban ƙasan cikin wani rubutu a shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi abu 1 da ba zai lamunta ba a Najeriya

IBB ya nesanta kansa da kalaman da aka jingina masa
Janar Ibrahim Babangida na son mulkin dimokuradiyya ya dore a Najeriya Hoto: @SearchmediaMX
Asali: Twitter

Shafin mai suna @General_Ibbro a manhajar X (wacce a baya aka fi sani da Twitter), ya ce Ibrahim Badamasi Babangida ya fi son mulkin soja fiye da na dimokuraɗiyya, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me IBB ya ce kan dawowar mulkin soja?

Sai dai a cikin wata sanarwa da Mahmoud Abdullahi ya sanyawa hannu a madadin ofishin watsa labarai na tsohon shugaban ƙasan, ya ce ko kaɗan shafin ba nasa ba ne, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya bayyana cewa Ibrahim Badamasi Babangida yana nan a ƙudirinsa na ganin mulkin dimokuraɗiyya ya tabbata.

A cikin sanarwar ya yi nuni da cewa shafin ya sha rubuta kalaman ƙarya sannan ya danganta su ga tsohon shugaban ƙasan.

"Mun fahimci cewa shafin ya sake wallafa kalaman ƙarya inda yake cewa tsohon shugaban ƙasan ya ce Najeriya ta fi samun ci gaba a shekarun mulkin soja, dimokuraɗiyya ta mayar da ita baya."

Kara karanta wannan

Ana cikin anga zanga, Rundunar Sojoji ta sanar da kashe miyagu sama da 500 a Najeriya

"Muna son mu bayyana cewa shafin na X wanda na ƙarya ne ko sanarwar da aka yi a cikinsa, ba su kasance na Ibrahim Badamasi Babangida ba ne."
"Domin cire duk wani shakku, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) ya yi amanna cewa dimokuraɗiyyar Najeriya za ta ɗore kuma dole ne mu yi duk mai yiwuwa domin kare ta."

- Mahmoud Abdullahi

Ya nuna takaicinsa kan yadda suka kasa sanyawa a cire shafin na bogi, sannan ya gargaɗi jama'a da su daina yarda da duk wani rubutu daga shafin mai iƙirarin cewa yana faɗin ra'ayin tsohon shugaban ƙasan ne.

Karanta wasu labaran kan Janar IBB

"Yadda Babangida da Obasanjo suka nemawa Buhari alfarmar takara a zaben Shugaban kasa"

Tsohon shugaban kasa Janar IBB ya gano hanyar gyara Najeriya daga tushe

Tsadar rayuwa: Babangida ya gargadi Tinubu kan yiwuwar juyin mulkin soja a Najeriya? Gaskiya ya fito

Ra'ayin IBB kan mulkin soja

Kara karanta wannan

Wani malamin addini ya gayawa Tinubu gaskiya, ya fadi babbar matsalar gwamnatinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa a zamanin mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya ce yana da yaƙinin cewa ba za a sake samun katsalandan daga sojoji ba wanda zai kawo cikas ga dimokuradiyya a Najeriya.

Janar IBB ya ce zamanin da sojoji ke kutsa kai ciki harkokin siyasa ya zo ƙarshe saboda ƴan Najeriya sun ƙara gamsuwa ƙasar ta ci gaba da zama kasa mai bin tafarkin dimokuradiyya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng