“Babu Mai Hana Ni Darewa Sarauta”: Tsohon Gwamna Ya Sha Alwashi Kan Karaga
- Yayin da aka naɗa sabon Olubadan na Ibadan, tsohon gwamnan Oyo ya sha alwashin darewa sarautar a nan gaba
- Rashidi Ladoja ya ce babu mai hana shi samun sarautar idan har ubangiji ya ƙaddara masa haka a rayuwarsa
- Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Oyo da ta shude da Gwamna Seyi Makinde sun kawo sauye-sauye a tsarin sarautar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja ya yi magana kan neman sarautar Olubadan mai daraja a jihar.
Ladoja ya ce idan yana raye babu wanda zai hana shi darewa sarautar Olubadan komai daren dadewa a jihar.
Oyo: Ladoja ya sha alwashin zama Olubadan
Tsohon gwamnan ya bayyana haka a jiya Lahadi 4 ga watan Agustan 2024 a cikin wata sanarwa, cewar the Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ladoja ya amince da karbar sandan sarauta ta musamman a matsayin wani mataki na zama Olubadan a gaba.
"Zan karbi sandar sarautar idan wannan shi ne ya hana ni zama Olubadan na kasar ibadan."
- Rashidi Ladoja
Yadda gwamnatoci suka sauya tsarin sarautar Olubadan
Ladoja ya sha takun-saka da tsohon gwamnan jihar, Abiola Ajimobi wanda ya yi kokarin kawo sauyi a tsarin sarautar, cewar Punch.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Ladoja shi ne a kan layi wanda zai gaji sarautar Olubadan duk da sauya tsare-tsaren da Gwamna Seyi Makinde ya yi a yanzu.
Matakin Gwamna Makinde ya kawo rudani a jihar inda ake ganin yana da wata manufa.
Tsohon gwamnan ya ce babu mai iya hana shi zama Olubadan na gaba idan har Allah ya ƙaddara masa hakan.
Zanga-zanga: Gaskiya kan hari a gidan Buhari
Kun ji cewa Masarautar Daura ta yi magana bayan jita-jitar cewa masu zanga-zanga sun dira gidan sarkin da na Muuhammadu Buhari.
An ruwaito cewa wasu masu zanga-zanga sun yi dafifi a gidan tsohon shugaban kasa da kuma Sarkin Daura a jihar Katsina.
Kakakin Sarkin Daura, Usman Ibrahim Yaro ya musanta cewa matasan sun taba gidajen Buhari da na sarkin inda ya ce wucewa suka yi.
Asali: Legit.ng