Zanga Zanga: Wole Soyinka Ya Fadi Kuskuren Tinubu bayan Jawabinsa kan Zanga Zanga
- Farfesa Wole Soyinka ya ce jawabin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai tabo batun zaluncin ‘yan sanda kan masu zanga-zangar yunwa ba
- Shahararren marubucin mai shekaru 90 a duniya ya yi Allah wadai da yadda kasar ke ci gaba ta fuskar muzgunawa masu zanga zanga
- Wanda ya lashe kyautar Nobel ya yi kira ga hukumomin tsaro da su yi amfani da wasu hanyoyin magance zanga-zanga ba ta karfin tsiya ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Farfesa Wole Soyinka, wanda ya samu lambar yabo ta Nobel, ya mayar da martani ga jawabin da Shugaba Bola Tinubu ya yi game da zanga-zangar yunwa da ake yi a kasar.
Farfesa Soyinka ya caccaki jawabin Shugaba Tinubu kan rashin magana kan cin zarafin masu zanga-zangar da jami’an tsaro suka yi.
Marubucin littattafai, dan shekaru 90 ya nuna damuwarsa kan yadda Tinubu ya yi watsi da wannan muhimmin batu, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Soyinka ya ga kuskuren jawabin Tinubu
Ya ce jawabin Tinubu bai yi magana kan zaluncin ‘yan sanda kan masu zanga-zangar ba kuma ya yi gargadin yiwuwar juyin juya hali idan har irin hakan ta ci gaba da faruwa.
Wani bangare na sanarwar marubucin ya ce:
“Abin da ya fi damu na shi ne, tabarbarewar da gwamnatin kasar ta yi kan abin da ya shafi zanga-zanga, bangaren da jawabin shugaban ya gaza tabawa.
"Ma damar za a ba jami'an jami’an tsaro makamai su rika cin zarafin wadanda ke gabatar da wani abu da ya shafi 'yancin su, to hakan zai haifar da wani yanayi na bacin rai da ramuwar gayya."
Zanga-zanga: Soyinka ya caccaki jami'an tsaro
Sanarwar Wole Soyinka ta ci gaba da cewa:
"A rika amfani da harsashi mai rai kan masu zanga zanga, wannan babban al'amari ne. Hatta amfani da barkon tsohuwa yana zuwa da ayar tambaya, ya sabawa tsarin 'yancin zanga-zangar lumana.
"Yana haifar da tauye 'yancin kai, wato a koma kamar mulkin mallaka."
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Soyinka ya kuma bukaci hukumomin tsaro da su yi amfani da wasu hanyoyi na magance zanga-zangar lumana ba wai ta karfin tsiya ba.
'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami’an ‘yan sandan kasar nan sun tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga da borkonon tsohuwa a filin Eagle da ke babban birnin tarayya Abuja.
‘Yan sandan sun bayyana cewa sun dauki matakin ne domin tabbatar da umarnin kotu na cewa masu zanga-zanga su tsaya a filin wasa na Moshood Abiola.
Asali: Legit.ng