'Yan Daba Sun Farmaki Wurin Ibada Ana Cikin Zanga Zanga, Sun Tafka Barna
- Wasu miyagun ƴan daba sun yi amfani da lokacin yin zanga-zanga domin tafka ta'asa a garin Daura da ke jihar Katsina
- Ƴan daban sun yi dirar mikiya cikin cocin Living Faith da ke Daura inda suka kwashe kayayyaki na miliyoyin Naira
- Faston da ke kula da cocin ya bayyana cewa ƴan daban sun shiga cocin ne a ranar da aka fara zanga-zangar adawa da halin ƙunci a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Wasu ƴan daba sun kai farmaki wata coci mai suna Living Faith da ke ƙaramar hukumar Daura a jihar Katsina.
Ƴan daban a yayin farmakin sun sace kujeru kusan 205, da kayan kaɗe-kaɗe, da wasu kayayyaki na miliyoyin naira.
Yadda ƴan daba suka yi ɓarna a Katsina
Ƴan daban sun dira a cocin ne yayin da ake zanga-zangar #Endbadgovernance a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Faston da ke kula da cocin, David Jatau, ya bayyana cewa sun kasa gudanar da ibada a ranar Lahadi saboda ƴan daban sun kwashe dukkanin wani abu da ke cikin cocin a lokacin zanga-zangar, rahoton The Nation ya tabbatar.
"Muna da jami'an tsaro biyu da ke aiki a cocin, ɗaya yana bakin aiki yayin da ɗayan ya tafi hutu. Lokacin da aka fara zanga-zangar da misalin ƙarfe 10:00 na safe, ƴan daban kawai sai suka taho cocin."
"Da yawa daga cikinsu suna cikin Keke Napep, sannan suka fasa ƙofofi da gilasai suka shige cikin cocin."
"Sun kwashe komai da ke cikin cocin da suka haɗa da agogon bango, kayan kiɗa, kujerar fasto, kujerun roba da kwamfuta. Sun lalata komai."
- David Jatau
An sanar da ƴan sanda
Ya ƙara da cewa cocuka uku aka yi hari amma ƴan daban sun yi nasara ne kawai a cocin Living Faith Church da Deeper Life Church, amma sun kasa shiga cocin Anglican Church saboda ƙofar cocin na da ƙarfi sosai.
Ya bayyana cewa sun gayawa ƴan sanda da sojoji abin da ya faru, inda a jiya suka sanar da su cewa sun kama wasu mutane.
Tinubu ya buƙaci a dakatar da zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zanga-zangar #Endbadgovernance da ake yi a faɗin ƙasar nan.
Shugaba Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da ke zanga-zangar adawa da gwamnatinsa da su gaggauta dakatar da zanga-zangar su fito domin a tattauna.
Asali: Legit.ng