Bayan Legas: Matasan Wata Jihar Kudu Sun ji Kiran Tinubu, Sun Dakatar da Zanga Zanga

Bayan Legas: Matasan Wata Jihar Kudu Sun ji Kiran Tinubu, Sun Dakatar da Zanga Zanga

  • Awanni bayan jawabin Shugaba Bola Tinubu, matasa sun dakatar da zanga-zangar da suke yi a Edo domin amsa kiran shugaban kasar
  • Matthew Ojeikere, daya daga cikin jagororin zanga-zangar a Edo, ya bukaci Tinubu da ya cika alkawuran da ya dauka a jawabinsa
  • Jagoran masu zanga-zangar ya kuma bayyana cewa ‘yan Najeriya na so ci gajiyar shugabanci na gari da kuma kawo karshen wahalhalu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Awanni bayan jawabin Shugaba Bola Tinubu na kai tsaye a ranar Lahadi, matasa sun dakatar da zanga-zangar da suke yi a Edo domin amsa kiran shugaban kasar.

Masu zanga-zangar, wadanda suka fara a ranar Lahadi, 1 ga Agusta a Ring Road da ke Benin da kewaye, sun dakatar da zanga-zangar bayan jawabin Tinubu na karfe 7:00 na safiya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

Matasa sun dakatar da zanga-zanga a Edo bayan jawabin Tinubu
Matasa sun mika bukata ga Tinubu yayin da suka dakatar da zanga-zanga a Edo. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Matasa sun dakatar da zanga-zanga

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, matasan sun cire babbar rumfar zanga-zanga da suka kafa a Ring Road, kusa da gidan sarkin Benin, Omo N'Oba N'Edo Uku Akpolokpolo, Oba Ewuare II.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan sun kuma janye shingen da suka sanya kan titin Ring Road domin ba masu ababe hawa damar wucewa sabanin lokacin da ake zanga-zangar.

An ce 'yan sanda sun kasa sun tsare domin tabbatar da cewa an wanzar da doka da oda.

An kuma ruwaito cewa har zuwa karfe 11:30 na safiyar Lahadi, akwai shinge a yankin kamfanin Mat-Ice-Fast-food da ke kan titin Ekenwan.

"Bukatar masu zanga-zanga" - Ojeikere

Haka zalika, an ga matasa na tunkarar jami'an tsaro duk da cewa suna dauke da matakai a kusa da matsugunnin jami'ar Benin (UNIBEN) a lokacin da suke zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Kiristoci sun ba Musulmai masu sallar Juma'a kariya ana tsaka da zanga zanga

Matthew Ojeikere, daya daga cikin jagororin zanga-zangar a Ring Road, ya bukaci Shugaba Tinubu da ya cika alkawuran da ya dauka yayin gabatar da jawabinsa.

Jagoran masu zanga-zangar ya kuma bayyana cewa ‘yan Najeriya ba wai suna neman abin da ba zai yiwu ba ne, sai dai suna so ci gajiyar shugabanci na gari da kuma kawo karshen wahalhalun da ake fama da su.

Legas: Matasa sun dakatar da zanga-zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani bangare na matasan da ke adawa da 'mummunar gwamnati' a yankin Ojata da ke Legas sun yi kira da a dakatar da zanga zanga.

Sun sanar da 'yan sanda wannan matakin da suka dauka tare da cewar za su fice daga filayen da suka gudanar da zanga-zangar wanda ke kawo karshen gangamin kenan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.