Bidiyo: Jawabin Tinubu ya Fara Tasiri, Matasa Sun Janye Zanga Zanga a Birnin Legas

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya Fara Tasiri, Matasa Sun Janye Zanga Zanga a Birnin Legas

  • Wani bangare na masu zanga-zangar adawa da 'mummunar gwamnati' a yankin Ojata da ke Legas sun yi kira da a dakatar da gangamin
  • Kiran ya zo ne bayan jawabin da Shugaba Bola Tinubu ya yi a safiyar Lahadi, inda ya bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu
  • Sai dai wani bangare na masu zanga-zangar sun ce ba za su koma gida ba har sai shugaban kasar ya biya bukatunsu ba wai a iya magana ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ojota, Legas - Biyo bayan jawabin kai tsaye da Shugaba Bola Tinubu ya yi ga 'yan Najeriya, masu zanga-zanga a Ojota da ke Legas sun sanar da kawo karshen gangamin.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya gama jawabi": Miyagu sun watsa masu zanga zanga, sun fadi dalili

Sun sanar da 'yan sanda wannan matakin da suka dauka tare da cewar za su fice daga filayen da suka gudanar da zanga-zangar wanda ke kawo karshen gangamin kenan.

Jagororin matasa sun yi kira da a janye zanga-zanga haka nan
Legas: Jagororin matasa sun nemi a ba da lokaci domin duba jawabin Tinubu. Hoto: Pierre Favennec/AFP
Asali: AFP

Shugabanni sun janye zanga-zanga a Legas

Wani ma'abocin shafin X, @Mr_JAGs ne ya wallafa bidiyon a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin masu zanga-zangar na ganin cewa dakatar da ita zai ba da dama ta yiwa jawabin shugaban kasar karatun ta-nutsu domin sanin ko akwai wata makama a ciki.

"Tun da Shugaba Tinubu ya yiwa kasa jawabi, za mu ba da lokaci domin yin bitar maganganunsa," a cewar wani shugaban masu zanga-zangar.

Legas: Wani bangare yaki janye zanga-zangar

Duk da wannan kira, wasu daga cikin masu zanga-zangar sun dage kan cewa lallai ba za su matsa ko nan da can ba, har sai an biya bukatunsu ba wai a iya magana kurum ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Abubuwa 9 masu muhimmanci daga jawabin Shugaba Tinubu ga 'yan Najeriya

"Ba za mu koma gida ba. Har yanzu shugaban kasar bai biya bukatunmu ba," wani daga cikin masu zanga-zangar ya yi nuni.

Jaridar The Nation ta ce har yanzu akwai dar dar a Ojota, yayin da aka ga 'yan sanda masu tarin yawa a inda ake gudanar da zanga-zangar wadanda ke kira da ayi maslaha.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Abubuwa 9 game da jawabin Tinubu

Tun da fari, Legit Hausa ta tattaro wasu muhimman abubuwa tara daga cikin jawabin da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar ga 'yan Najeriya a safiyar ranar Lahadi.

Shugaban kasar wanda ya yi magana kan zanga-zangar da ake gudanarwa a kasar ya ce gwamnarinsa ta dauki matakan kawo karshen radadin da 'yan kasar ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.