"Tinubu Ya Gama Jawabi": Miyagu Sun Watsa Masu Zanga Zanga, Sun Fadi Dalili

"Tinubu Ya Gama Jawabi": Miyagu Sun Watsa Masu Zanga Zanga, Sun Fadi Dalili

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu miyagu sun tarwatsa masu zanga-zanga a yankin Ojota da ke jihar Lagos a Najeriya
  • Matasan sun tarwatsa masu zanga-zangar da cewa ai Shugaba Bola Tinubu ya riga ya yi jawabi ga 'yan kasar kan matsalar
  • Sai dai masu zanga-zangar sun ce babu wani korafin da suke da ita wanda shugaban ya dauki mataki a kai a jawabin na shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Miyagu sun yi kwantan bauna inda suka tarwatsa masu zanga-zanga a jihar Legas yayin da aka shiga rana ta hudu.

Matasan sun watsa masu zanga-zangar a wurin shakatawa na Gani Fawehunmi da ke yankin Ojota a jihar.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

Miyagu sun watsa masu zanga-zanga a Lagos bayan jawabin Tinubu
Awanni bayan jawabin Bola Tinubu, matasa sun watsa masu zanga-zanga. Hoto: @PoliceNG.
Asali: Twitter

Jawabin Tinubu: An samu sabani a Lagos

Channels TV ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na safe yayin da aka samu hargitsi a wurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu sabani ne tsakanin wadanda suka shirya zanga-zangar da ke Ojota inda miyagun suka samu damar watsa su.

Wani lauya mai suna JP ya iso wurin domin yin jawabi ga masu zanga-zangar da cewa su watse saboda Bola Tinubu ya yi jawabi.

Sai dai wasu gungu a wurin da wani dattijo mai shekaru 70 ke jagoranta mai suna Adegboyega Adeniji ya ki amincewa da cewa jawabin bai shafi matsalolinsu ba.

Adegboyega wanda ke jagorantar Peace Action Transformation ya ce babu mai hana su cigaba da zanga-zangar, cewar Punch.

'Yan sanda sun shiga tsakanin masu zanga-zanga

Rundunar 'yan sanda ta sanya baki inda ta ke jawabi ga wani bangare na masu zanga-zangar da su watse a wurin.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Abubuwa 9 masu muhimmanci daga jawabin Shugaba Tinubu ga 'yan Najeriya

Bayan jawabin 'yan sandan, wasu matasa sun bullo daga wani bangare da ake zargin an dauki nauyinsu inda suka tarwatsa su.

Daga bisani, sun sake dawowa inda suka kori duka masu zanga-zangar a Ojota kafin 'yan sanda su kwace ikon wurin.

Tinubu ya magantu kan tallafin mai

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan dawo da tallafin man fetur da ya jefa al'umma cikin kunci a Najeriya.

Shugaban ya ce cire tallafin ya zama dole duk da ya san halin kunci da hakan ya jefa 'yan Najeriya a ciki na tsawon lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.