Ana Cikin Zanga Zanga 'Yan Bindiga Sun Hallaka Wasu Masu Rike da Sarauta

Ana Cikin Zanga Zanga 'Yan Bindiga Sun Hallaka Wasu Masu Rike da Sarauta

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan hari a ƙauyen Umucheke Okwe da ke ƙaramar hukumar Onuimo a jihar Imo
  • A yayin harin ƴan bindiga sun hallaka shugaban ƙauyen tare da wasu masu unguwanni shida bayan sun buɗe musu wuta
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar harin inda ta ce tana bincike domin gano masu hannu a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Ƴan bindiga sun kai wani ƙazamin hari a jihar Imo inda suka kashe shugaban wani ƙauye tare da wasu masu riƙe da sarautun gargajiya.

Ƴan bindigan sun hallaka shugaban ƙauyen Umucheke Okwe da ke ƙaramar hukumar Onuimo, Hyginus Ohazurike, a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun dira gidan Buhari a Daura, bayanai sun fito daga Katsina

'yan bindiga sun kai hari jihar Imo
'Yan bindiga sun hallaka mutane a jihar Imo Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Ƴan bindigan sun kuma hallaka masu unguwanni shida a ƙauyen a yayin harin da suka kai, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai hari a Imo

Wani ɗan asalin ƙauyen wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce ƴan bindigan sun kawo harin ne cikin wata mota lokacin da mutanen suke gudanar da wani taro a ƙauyen, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

"Wasu ƴan bindiga sun hallaka shugaban ƙauyen Umucheke Okwe da wasu masu unguwanni shida."
"Shugaban ƙauyen yana yin taro ne da masu unguwannin a shagonsa da ke cikin kasuwar ƙauyen lokacin da ƴan bindigan suka iso."
"Suna zuwa kawai sai suka buɗe wuta inda suka hallaka dukkanin shugabannin tare da cinnawa wajen wuta. Dukkanin shugabannin sun mutu a sakamakon harin."

- Wata majiya

Majiyar ta ƙara da cewa babu wanda ya san dalilin kawo harin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro da manoma a wani kazamin hari a Sokoto

Me hukumomi suka ce kan harin?

Shugaban ƙaramar hukumar Onuimo, Emeka Obi, ya tabbatar da aukuwar harin inda ya buƙaci jama'a da su kwantar da hankulansu.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye, a cikin wata sanarwa ya bayyana harin a matsayin aikin rashin imani.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano masu hannu a cikin lamarin.

Ƴan bindiga sun hallaka jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Karfen Sarki cikin ƙaramar hukumar Gudu ta jihar Sokoto inda suka hallaka mutum bakwai.

Ƴan bindigan sun hallaka jami'an rundunar tsaron jihar mutum biyar da wasu manoma mutum biyu bayan sun yi musu kwanton ɓauna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng