Zanga Zangar Adawa da ‘Mummunan Mulki’: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani ga Jawabin Tinubu

Zanga Zangar Adawa da ‘Mummunan Mulki’: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani ga Jawabin Tinubu

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya inda ya amince da koke-kokensu tare da bayyana shirye-shiryen gwamnatinsa na magance matsalolin
  • ‘Yan Najeriya sun mayar da martani kan jawabin Tinubu a shafukan sada zumunta, inda wasu ke nuna goyon baya yayin da wasu ke sukar shugaban
  • An samu ra'ayoyi mabambanta, inda wasu ke kira da a kawo karshen zanga-zangar, wasu kuma na neman a dauki kwararan matakai domin rage yunwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A yayin da zanga-zangar adawa da 'mummunar gwamnati' ta shiga rana ta 4, Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga 'yan Najeriya a safiyar ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

Shugaban na Najeriya ya amince da korafe-korafen ‘yan Najeriya tare da bayyana shirin gwamnatinsa na magance su.

'Yan Najeriya sun yi martani ga jawabin Shugaba Bola Tinubu kan zanga zanga.
Ra'ayoyi sun bambanta game da jawabin da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar kan zanga-zanga. Hoto: KOLA SULAIMON/AFP
Asali: Getty Images

Ga yadda wasu ‘yan Najeriya suka mayar da martani ga jawabin shugaban kasar:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na goyi bayan cire tallafin fetur" - Omokri

Tsohon hadimin shugaban kasa Reno Omokri, @renoomokri, ya wallafa a shafinsa na X cewa:

“Na ba da cikakken goyon baya ga cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi. Wannan manufar tana cikin tsarin mu a matsayinmu na jam’iyyar PDP.
"A matsayina na amintaccen Shugaba Jonathan na wancan lokacin, na kuma ba da shawarar a cire tallafin tun a shekarar 2012.

"Tinubu ya damu da 'yan kasa" - Okezie

Pst Okezie, @Onsogbu, ya bayyana cewa:

"Mu kara hakuri da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa domin idan kun saurari duk abinda ya fada a nan, za ku gane cewa a koda yaushe yana da muradin 'yan Najeriya a zuciyarsa.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Tinubu sun yi kishiyar zanga zanga a Kano, su na goyon bayan gwamnati

"Ni da iyalina za mu ci gaba da dakon ci gaban da shugaban zai kawo kuma muna tare da shi."

"Lokaci dakatar da zanga-zanga ya yi" - Offor

David Offor, @DavidsOffor, ya fadi ra'ayinsa:

"Lokaci ya yi da za a kawo karshen zanga-zangar ta hanyar lalama ko akasin haka. Shugaban ya yi jawabi ga al'ummar kasa, ba za a iya samun fiye da haka ba.
"Duk wanda aka gani har yanzu yana kan titi yana zanga zanga to yana yin haka ne saboda dalilai na Siyasa. Lokaci ya yi da za a baiwa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu damar gyarawa."
"Hukumomin tsaro su tabbatar da cewa zuwa gobe 'yan Najeriya za su koma yadda suke rayuwa a baya. Ba za mu iya barin wasu su ci dunduniyar kasarmu ba."

"Menene makomar 'yan Npower?" - Murtano

A ra'ayin Ahmad Murtano, @Murtadohadewale:

"Ya batun dakatar da shirye-shiryen zuba hannun jari na kasa? Menene makomar wanda ya ci gajiyar Npower amma yake bin bashin watanni 9."

Kara karanta wannan

"Muna can muna cin abinci," Shugaban Majalisa ya ta da ƙura kan zanga zanga da ake shirin yi

"Gwamnatin Tinubu ba ta da tausayi" - Yusuff

LaGoS LaWyeR, @omodolapoyusuff, ya ce:

"Jawabin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayi a yau ya nuna yadda gwamnati ke nuna rashin tausayi ga halin da talaka ke ciki
"Mutanen da ya ce yana wakilta ba su da wata shaida a kan nasarorin da aka lissafa, illa ma akasin abin da ya zayyana ne 'yan Najeriya ke fuskanta."

Abubuwa 9 daga jawabin Shugaba Tinubu

Tun da fari, Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga 'yan Najeriya a ranar Lahadi game da zanga-zangar da ake yi, ya fadi matakan da gwamnatinsa ta dauka domin cire 'yan kasa daga tsadar rayuwa.

Daga cikin jawabin da Shugaba Tinubu ya yi, Legit Hausa ta tattaro wasu muhimman abubuwa tara da ya kamata 'yan Najeriya su lura da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.