Zanga Zanga: Tinubu Ya Dauki Alkawari 1 Yayin da Ya Fallasa Shirin Wasu 'Yan Siyasa
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zargi wasu tsirarun 'yan siyasa da rura wutar zanga-zanga domin kawo hargitsi da tashin hankali a kasar
- Shugaba Tinubu wanda ya yi jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya ya nuna takaici kan yadda aka kashe mutane a Kano, Kaduna da sauran jihohi
- Tinubu ya lashi takobin kare dukiyoyi da rayukan 'yan Najeriya daga makiricin wadannan tsirarun 'yan siyasar da yake magana a kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shuagaba Bola Tinubu ya yi magana kai tsaye ga 'yan Najeriya game da zanga-zangar adawa da gwamnatinsa da ake yi wadda ya ce ta koma ta 'tashin hankali.'
Shugaba Tinubu ya nuna takaicinsa kan yadda zanga-zangar ta kai ga rasa rayuka, lalatawa da kuma sace dukiyoyin jama'a a sassan kasar.
Tinubu ya magantu kan kisan matasa
A rubutaccen jawabin da shugaban kasar ya yi, wanda mai tallafa masa kan watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X, Tinubu ya ce akwai shirin 'yan siyasa a zanga-zangar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da fari dai shugaban kasar ya yi takaicin rasa rayukan matasan da aka yi a jihohin Borno, Jigawa, Kano, Kaduna da ma sauran jihohi da kuma sacewa da lalata dukiyoyin jama'a.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa wannan barnar da aka yi a lokacin zanga-zangar ta sake mayar da kasar baya a yayin da take kokarin ganin cewa ta je tudun-mun-tsira.
Zanga-zanga: Tinubu ya zargi 'yan siyasa
A rubutaccen jawabin shugaban kasar, Tinubu ya ce akwai wasu tsirarun mutane wadanda suka saka manufar siyasarsu a cikin wannan zanga-zangar.
Shugaba Tinubu ya ce manufar 'yan siyasar ita ce su sanya tashin hankali da raba kan 'yan kasar.
Sai dai shugaban kasar ya lashi takobin dawo da zaman lafiya yayin da kuma zai kara riko da rantsuwar kare rayuka da dukiyoyin jama'ar kasar da ya yi a lokacin kama aiki.
Ana zargin APC da kwace zanga-zanga
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar Edolites for Peace and Progress (EPP) karkashin Adesua Odigie ta zargi APC da yunkurin kwace zanga-zangar da ake yi a Edo.
Kungiyar ta yi zargin cewa APC na shirin hurowa gwamnatin PDP a jihar wuta ta hanyar kwace zanga-zangar domin cimma wata manufar siyasa da ka iya kai ga tashin hankali.
Asali: Legit.ng