An Samu Babbar Matsala: ’Yan Sanda Sun Ba Masu Zanga-Zanga Shawari Mai Daukar Hankali

An Samu Babbar Matsala: ’Yan Sanda Sun Ba Masu Zanga-Zanga Shawari Mai Daukar Hankali

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce, abu ne mai kyau masu zanga-zangar yaki da zaluncin gwamnati su gaggauta janyewa
  • Wannan na zuwa ne bayan ‘yan sanda sun kame mutane sama da 681 a ranakun Alhamis da Juma’a na farkon watan Agusta
  • Wata sanrwar da rundunar ta fitar ya bayyana dalilan da suka sa rundunar bayyana bukatar a gaggauta janye zanga-zangar da ta sauya akala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bukaci masu zanga-zangar yaki da gwamnatin da ta jefa al’umma yunwa su gaggauta janyewa nan take.

‘Yan Najeriya sun fara fita zanga-zangar lumana a kwanakin nan, inda suke bayyana kokensu kan yanayin da ake ciki a kasar nan na yunwa da fatara bayan hawan shugaba Bola Ahmad Tinubu mulkin kasar.

A dakata da zanga-zanga haka, inji 'yan sanda
'Yan sanda sun shawarci a dakata da zanga-zanga | Hoto: @PoliceNG
Asali: UGC

Wata sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sandan kasa, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce ya kamata a janye zanga-zangar ta kwanaki 10 tun da alamu sun nuna ta koma rikici da sace-sace.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan sandan Kano sun tashi tsaye, an fara bin gida gida neman kayan sata

Ana yada rahotannin karya a kanmu, ‘yan sanda

Rundunar ta kuma yabawa jami’anta da sauran jami’an tsaro a kasar bisa aikin ji da masu tada zaune tsaye a lokacin zanga-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani yankin sanarwar na cewa:

“A bayyane yake zanga-zangar da ake yi ta koma rikici.
“Don haka muke shawartar ‘yan kasa masu bin doka da oda da su gaggauta ficewa tare da janye ci gaba da zanga-zangar. Wannan shawari ya zama dole duba da barnar da aka tafka a kwanaki biyu na zanga-zangar.
“A hankalce ya kamata masu zanga-zangar lumana su janye daga zanga-zangar da ta koma tashin-tashina.”

Za mu ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya, ‘yan sanda

Rundunar ta kara da cewa:

“A wannan yanayin, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kuma jaddada jajircewarta na aikin doka cikin kwarewa tare da tabbatar da doka da oda tare da yakar tashin-tashina a duk fadin kasar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan sanda na kokarin kakkabe miyagu, an kama 'yan daba 50 a Katsina

“Rundunar ‘yan sandan Najeriya da su kauracewa duk wasu rahotanni da bayanai na karya da ake yadawa game jami’ai a lokacin zanga-zangar.”

Dalilin da yasa dattijo ya fita zanga-zanga

A bangare guda, Bashir Alhassan haifaffen garin Kano ne wanda ya ga ji kuma ya ga yau, amma ya ce bai taba ganin kunci irin na yanzu ba.

Dattijon da aka Haifa a garin Diso a karamar hukumar Gwale a jihar Kano, ya koka game da yadda aka shiga matsancin hali a Najeriya.

A zantawarsa da Legit a ranar Juma’a, Malam Bashir Alhassan mai shekara 66 a duniya ya fada mana dalilinsa na shiga zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.