An Shiga Fargaba da Masu Zanga Zanga Suka Tare Tawagar Motocin Gwamna a Najeriya
- Yayin da ake cigaba da zanga-zanga, matasa sun tare tawagar motocin gwamnan jihar Rivers a yau Asabar 3 ga watan Agustan 2024
- Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnan ya fito ya yi musu jawabi da safiyar yau Asabar a birnin Port Harcourt da ke jihar
- Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta uku a zanga-zanga yunwa da halin kunci da ake ciki a fadin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Masu zanga-zanga sun tare tawagar motocin Gwama Siminalayi Fubara na jihar Rivers.
Lamarin ya faru ne da safiyar yau Asabar 3 ga watan Agustan 2024 a birnin Port Harcourt da ke jihar.
Rivers: Masu zanga-zanga sun tare tawagar gwamna
The Nation ta tattaro cewa masu zanga-zangar sun dauki matakin ne domin bukatar gwamnan ya sauko domin yin magana da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano dubban masu zanga-zanga sun cika titunan suna ihu tare da daga korayen ganye yayin nuna rashin jin dadinsu.
Daga bisani tawagar gwamnan ta yi nasarar wucewa bayan wani lokaci inda aka cigaba da zanga-zanga, cewar Channels TV.
An shiga rana ta uku a zanga-zanga
Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta uku a zanga-zanga wanda aka fara ranar Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.
Matasan na zanga-zanga domin neman gwamnati ta dauki matakan gaggawa game da halin kunci da ake ciki.
Rahotanni sun tabbatar da cewa a yau rana ta uku ana cigaba da zanga-zangar lumana a birnin Port Harcourt.
Jami'an DSS sun tarwatsa masu zanga-zanga
Kun ji cewa jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Abuja inda suka kutsa cikin filin wasa na MKO Abiola.
Lamarin ya jawo raunata mutane da dama cikin har da 'yan jaridu da sauran jama'a da suka yi dafifi a birnin domin zanga-zanga.
Ana zargin jami'an tsaron farin kaya na DSS ne suka yi ta harbi kan me uwa-da-wabi domin hana su taruwa a wurin da ake zanga-zangar.
Asali: Legit.ng