Rana Ta 3: Jami'an Tsaro Sun Cafke 'Yan Jarida da Masu Zanga Zanga
- Jami'an tsaro sun mamaye wurin da matasa ke gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja a ranar Asabar
- Jami'an tsaron aun hana masu zanga-zangar amfani da filin wasa na Moshood Abiola inda suka tarwatsa mutanen da suka taru a wajen
- Daga baya sun riƙa bi suna cafke mutanen da ke wajen filin wasan ciki har da ƴan jarida masu ɗauko rahotanni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jami’an tsaro sun mamaye filin wasa na Moshood Abiola, wurin da ake gudanar zanga-zangar adawa da halin ƙunci da yunwa a Abuja, babban birnin Najeriya.
Masu zanga-zangar sun buƙaci yin amfani da dandalin Eagle Square domin gudanar da zanga-zangar amma an hana su shiga.
Jami'an tsaro sun cafke masu zanga-zanga
Jami'an tsaron sun kuma cafke masu zanga-zanga da ƴan jaridar da ke a wajen filin wasan Moshood Abiola, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dai samu tsaiko a zanga-zangar da sanyin safiyar ranar Asabar saboda rashin fitowar mutane sosai.
Sai dai daga baya wasu daga cikin masu zanga-zangar sun fara yin dafifi a wajen filin wasan.
Ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga
Ba su shafe sa'a guda ba a wajen lokacin da ƴan sandan da ke wajen suka yi ta harbi tare da harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa su.
Bayan an tarwatsa su, wata tawagar ta sake taruwa, amma saidai a wannan karon ƴan sandan ba barkonon tsohuwa kawai suka harba ba, har da cafke duk wanda suka ritsa da shi ciki har da ƴan jarida.
Ƴan jaridar da ke cikin mutanen da aka cafke, sai da suka nuna shaida kafin a sake su tare da ba su umarnin su yi gaggawar barin wajen.
DSS sun cafke jagororin zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta cafke jagororin zanga-zangar nuna adawa da halin matsin tattalin arziƙi da rashin tsaro da aka gudanar a jihar Katsina.
Kabir Shehu Yandaki da Habibu Ruma, shugabannin zanga-zangar "Struggle for Good Governance" an gayyace su zuwa ofishin DSS da ke Katsina, inda daga bisani aka tsare su.
Asali: Legit.ng