Jami’an DSS Sun Yi Ta Harbin Masu Zanga Zanga a Abuja, an Yi Barna

Jami’an DSS Sun Yi Ta Harbin Masu Zanga Zanga a Abuja, an Yi Barna

  • Yayin da ake cigaba da zanga-zanga a birnin Abuja, jami'an tsaron farin kaya sun yi ta harbin matasa domin tarwatsa su
  • Ana zargin jami'an da tarwatsa 'yan jaridu wanda ya yi sanadin fasa motar wani daga cikin wakilan Premium Times
  • Hakan na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta uku a zanga-zangar da ake yi kan halin kunci da ake ciki a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Abuja inda suka kutsa cikin filin wasa na MKO Abiola.

Lamarin ya jawo raunata mutane da dama cikin har da 'yan jaridu da sauran jama'a da suka yi dafifi a birnin domin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Rana Ta 3: Masu zanga zanga sun yi takansu yayin da jami'an tsaro suka buɗe wuta

An watsa masu zanga-zanga da harbe-harbe a Abuja
Jami’an Tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Abuja. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Zanga-zanga: An yi ta harbi a Abuja

Punch ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a yau Asabar 3 ga watan Agustan 2024 yayin da jami'an tsaron suka yi ta harbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zanga-zanga sun sake taruwa ne bayan watsa su da jami'an tsaro suka yi a filin wasa na MKO Abiola, cewar AIT News.

Ana zargin jami'an tsaron farin kaya na DSS ne suka yi ta harbi kan me uwa-da-wabi domin hana su taruwa a wurin da ake zanga-zangar.

Dalilin haka masu zanga-zangar suka fantsama cikin daji kusa da filin wasan domin tsira da rayukansu.

An farmaki 'yan jarida da ke wurin

Daga bisani jami'an tsaron da suka rufe fuskokinsu sun juyo kan 'yan jarida da suke daukar rahoto a gefe guda.

Zuwansu ke da 'yan jaridun suka watse inda harsasai suka fasa motar wakilin gidan jaridar Premium Times da ke gefe .

Kara karanta wannan

Rana ta 3: Gwiwar masu zanga zanga ta fara sanyi, jama'a ba su fito a Abuja ba

Sannan an farfasa motocin wasu masu wucewa ta wurin yayin da lamarin ya rikide zuwa karamin tashin hankali.

Sanata ta musanta hannu a zanga-zanga

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ireti Kingibe ta yi martani bayan zarginta da hannu a cikin zanga-zangar da ake yi a Najeriya.

Sanata Kingibe ta musanta labarin inda ta ce wani tsohon bidiyo ne ake yadawa da ya kai kimanin makwanni shida da daukarsa.

Wannan na zuwa ne bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce jami'an tsaro sun gano Sanata da ke daukar nauyin zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.