Zanga Zanga: Duk da Barkewar Rikici, Gwamna Ya Fadi Dalilin Kin Kulle Mutane a Gida

Zanga Zanga: Duk da Barkewar Rikici, Gwamna Ya Fadi Dalilin Kin Kulle Mutane a Gida

  • Gwamnan jihar Gombe ya yi magana kan zanga-zangar da aka gudanar a jihar a ranar Alhamis wacce aka samu hatsaniya a ciki
  • Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce bai sanya dokar hana fita ba ne a jihar saboda kada ya ƙara jefa mutane cikin wahala
  • Ya nuna cewa ba ya adawa da zanga-zangar lumana amma ba zai bari a karya doka da oda ba a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana dalilin da ya sa gwamnati ba ta sanya dokar hana fita a jihar ba yayin zanga-zanga ranar Alhamis.

A yayin zanga-zangar ta lumana dai wasu ɓata-gari sun yi kutse inda suka tafka ɓarna.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗage dokar zaman gida, ya tabbatar da tashin bom ya halaka mutum 16

Gwamna Inuwa ya ki sanya dokar hana fita a Gombe
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi magana kan zanga-zanga a Gombe Hoto: @governor_Gombe
Asali: Twitter

A jihar Gombe wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi dafifi a ƙofar gidan gwamnati a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin ƙin sanya dokar kulle a Gombe

Sai dai, Gwamna Inuwa, a wata sanarwa da kakakinsa Ismaila Uba Misilli ya fitar ranar Juma’a a shafinsa na Facebook, ya ce ya yanke shawarar ƙin sanya dokar hana fita a jihar ne domin gujewa ƙara jefa mutane cikin wahala.

Gwamnan ya kuma koka da irin ɓarnar da aka yi a kan dukiyoyin jama’a a sakamakon zanga-zangar, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta amince da ayyukan da ke barazana ga zaman lafiyar jihar ba.

Me Gwamna Inuwa ya ce kan zanga-zanga?

Ya ƙara da cewa duk da cewa ba ya adawa da zanga-zangar lumana, ba zai amince da karya doka da oda ba.

"An san Gombe da zaman lafiya, kuma dole ne mu kiyaye hakan. Ba za mu ƙyale ayyukan da ke barazana ga zaman lafiyarmu ba. Ba mu da wata jiha sai Gombe."

Kara karanta wannan

"Arziki da talauci duk na Allah ne," Gwamna a Arewa ya yiwa masu zanga zanga nasiha

"Mun fahimci cewa ana fama da ƙalubale da wahalhalu a ƙasa, amma bai kamata mu bi hanyar tayar da rikici da ɓarna a jiharmu ba domin muna ɓacin ranmu."
"Bari na faɗi da kyau cewa ba mu yin adawa da zanga-zangar lumana. Mun san cewa dimokuraɗiyya da dokokinmu sun ba da ƴancin hakan, amma abubuwan da suka faru sun saɓa hakan tare da karya doka."

- Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya

An cafke jagororin zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta cafke jagororin zanga-zangar nuna adawa da halin matsin tattalin arziƙi da rashin tsaro da aka gudanar a jihar Katsina.

Kabir Shehu Yandaki da Habibu Ruma, shugabannin zanga-zangar "Struggle for Good Governance" an gayyace su zuwa ofishin DSS da ke Katsina, inda daga bisani aka tsare su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng