Zanga Zanga: 'Yan Sandan Kano Sun Tashi Tsaye, An Fara Bin Gida Gida Neman Kayan Sata

Zanga Zanga: 'Yan Sandan Kano Sun Tashi Tsaye, An Fara Bin Gida Gida Neman Kayan Sata

  • Yayin da jami'an tsaro a kasar nan ke ci gaba da kokarin dakile ayyukan 'yan daba daga zanga-zanga, an fara neman kayan sata a Kano
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta na bin gidajen jama'a, musamman wadanda ake zargi da ɗaukan kayan sata domin ƙwato su da mayarwa masu kayan
  • Zuwa wannan lokaci jami'an tsaro sun cafke mutane sama da 400 da ake zargi da yunkurin tayar da hatsaniya da satar kayan jama'a a lokacin zanga-zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.Assalamu Alaikum Sir.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan Kano ta fara daukar matakin gani wasu daga cikin kayan da jama'a su ka wawashe yayin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Yadda zanga zangar lumana ta zama silar barna da lalata dukiyoyin miliyoyi a Kano

A ranar farko na zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin tarayya ne wasu bata-gari su ka rika fasa shaguna tare da dibar kayan mutane da sunan sun ci ganima.

Kano map
An fara bin barayin kaya lokacin zanga-zanga har gida Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa an cafke matasa 326 da zargin satar kayan jama'a a fadin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a bi barayin zanga-zanga har gida

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jami'an rundunar 'yan sandan Kano za su fara bi gida-gida domin gano kayan jama'a da aka sace tare da boyesu.

Wasu bata-garin matasa sun fasa saboda ofishin hukumar sadarwa ta kasa inda su ka sace muhimman kaya na miliyoyin Naira.

Wata mai amfani da shafin Facebook ta wallafa bidiyon yadda jami'an 'yan sanda su ka rika bi gida-gida domin ƙwato kayan a unguwanni Yakasai da Durumin Zungura.

Kara karanta wannan

"Babu ruwanmu," Gwamnati ta kare kanta bayan tangardar intanet da rufe layukan waya

Zanga-zanga: Yan sanda sun kama matasa

A baya mun ruwaito cewa jami'an rundunar 'yan sandan Kano sun cafke matsa maza da mata da su ka rika dibar kayayyaki a ranar farkon gudanar da zanga-zanga.

A ranar Alhamis 1 Agusta ne aka fara zanga-zangar lumana a fadin Najeriya, sai dai abin ya rikice zuwa tashin hankali da sace-sace har da rasa rai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.